“Mayya Ce”: Matashi Ya Kama Mujiya a Gefen Janaretonsa a Bidiyo, Yana Shirin Siyarwa

“Mayya Ce”: Matashi Ya Kama Mujiya a Gefen Janaretonsa a Bidiyo, Yana Shirin Siyarwa

  • Wani matashi dan Najeriya ya baje kolin tsuntuwa ta musamman da wani abokinsa ya kama a kusa da janaretonsa
  • A cewarsa, ya zabi ciyarwa da kula da tsuntsuwar bayan ya gano cewa ana siyar da ita kan $4k (fiye da naira miliyan 3) a kasuwa
  • Jama’a sun yi martani kan bidiyonsa yayin da wasu suka yi ba’a cewa mujiyar daga kauyensa ne, wasu kuma sun ba shi shawara

Wani matashi dan Najeriya, Timi Trey, wanda ya tsorata bayan ya ga mujiya a gefen janaretonsa, ya sake sabon tunani.

Ku tuna cewa ya yada wani bidiyo cikin tsoro bayan ya ga tsuntsuwa a gefen janaretonsa sannan ya nemi wani ya dauke masa ita.

Matashi zai siyar da mujiyar da ya tsinta
“Mayya Ce”: Matashi Ya Kama Mujiya a Gefen Janaretonsa a Bidiyo, Yana Shirin Siyarwa Hoto: @timitrey
Asali: TikTok

A wani sabon ci gaba, Timi ya nuna aniyarsa na son siyar da mujiyar bayan ya yi ikirarin cewa farashinta ya kai $4k (fiye da naira miliyan 3) a kasuwa.

Kara karanta wannan

Ba Na Adawa Da Addinin Musulunci a Matsayina Na Ministan Abuja, Wike

A wani bidiyon TikTok, Timi da wani abokinsa sun ciyar da mujiyar soyayyiyar shinkafa da kaza a cikin roba. An garkame mujiyar a cikin wani kwali.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, Legit Hausa bata da tabbaci kan ainahin farashin mujiyan.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama’a sun yi martani kan tsuntsun da Timi ya kama

tboi36 ya ce:

“Har sai ka gama da gaba daya kudin da ke asusunka kafin ka san cewa tsuntsun bai da wani daraja.”

bibah ta ce:

“Don Allah ka ciyar da tsuntsun hatsi.
"1. Danyen gero, masara, gyada.
"2. Ka nema mata akulki mai kyau ba kwali ba.
"3. Ka samu likitan dabbobi ya yanke mata fukafuki don kada ta tashi.”

marostyles8 ya ce:

“Koda dai dangin mayu ce…baaaba ka siyar…mutum na farko a tarihi da ya siyar da mayya ko mutanen kauyensa don zama mai kudi.”

Kara karanta wannan

“Na Tsorata”: Wani Dan Najeriya Ya Koka Yayin da Ya Ci Karo Da Wata Halitta a Janaretonsa, Ya Saki Bidiyo

Amarya ta antayawa uwarginta tafasashen ruwa kan zargin maita a jihar Kwara

A wani labari na daban, an tsare wata matar aure mai shekaru 42, Lola Abdulsalam gidan ajiya da gyaran hali, a Illorin babban birnin Jihar Kwara, bisa zargin shekawa Uwargidanta, Bilkisu Abdulsalam ruwan zafi.

A ranar Juma'a ne yan sanda suka gabatar da Lola a gaban kotu bisa zargin laifuka guda biyu. Na farko shine zargin cin mutunci da kuma bata suna, wanda ya saba da sashe na 257 da kuma 292 na kundin penal code.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

iiq_pixel