Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar NAHCON
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya rushe shugabannin gudanarwa na hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON)
- Shugaban ƙasa ya kuma amince da naɗin Alhaji Jalal Ahmad Arabi a matsayin sabon shugaban hukumar har na tsawon shekara huɗu
- Shugaba Tinubu ya kuma umarci shugaban hukumar mai barin gado da ya tafi hutu na wata uku har ya zuwa lokacin da zai yi ritaya
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba ya amince da naɗin Alhaji Jalal Ahmad Arabi a matsayin shugaban hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON).
Sabon shugaban na hukumar NAHCON ya taɓa riƙe muƙamin babban sakatare a fadar gwamnatin tarayya, a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
Alhaji Arabi zai jagoranci hukumar NAHCON na tsawon shekara huɗu.
NAHCON: Tinubu ya sauke Kunle Hassan
A cewar wata sanarwa da Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban ƙasa ya fitar, Tinubu ya umurci shugaban hukumar mai barin gado, Alhaji Zikrullah Kunle Hassan da ya tafi hutun watanni 3 kafin ya yi ritaya “kamar yadda dokar ma'aikatan gwamnati (PSR) ta tanada 120243."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hutun zai fara aiki ne daga ranar Laraba, 18 ga watan Oktoban 2023, kuma zai ƙare a lokacin da zai yi ritaya daga aiki a ranar 17 ga Janairun 2023.
Sanarwar ta yi nuni da cewa Alhaji Jalal Ahmad Arabi, zai fara aiki a ranar 18 ga Oktoban 2023, a matsayin muƙaddashin shugaba, sannan sai fara aiki a matsayin shugaban hukumar daga ranar 17 ga watan Janairun 2024, har zuwa shekara huɗu.
Shugaba Tinubu ya kuma amince da rusa shugabannin gudanarwa na ukumar ta NAHCON.
Sanarwar ta ce, Shugaba Tinubu na sa ran sabbin shugabannin na NAHCON za su yi aiki cikin tsoron Allah tare da bin ƙa'idojin aiki kamar yadda Alkur’ani mai girma ya tanada.
Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Shugaban ICPC
A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabon shugaba wanda zai jagoranci hukumar yaƙi da cin hanci ta ICPC.
Shugaban ƙasar ya nada Dakta Musa Adamu Aliyu a matsayin sabon shugaban hukumar yayin da ya kuma naɗa Mista Clifford Okwudiri a matsayin sakataren hukumar.
Asali: Legit.ng