Matashiya Da Ita Kadai Iyayenta Suka Haifa Ta Mutu Kwanaki 12 Bayan Bikin Kammala Jami’a a Facebook
- Wata matashiya yar Najeriya ta kwanta dama a wani hatsari kwanaki 12 bayan ta yi bikin kammala jami'arta a Facebook
- Matashiyar, wacce ita kadai iyayenta suka haifa ta binne mahaifinta da ya rasu yan makonni da suka gabata, a watan Satumba
- Mutane sun garzaya shafin dalibar ta jami'ar tarayya da ke Otuoke don mika ta'aziyyarsu
Chidera John, wata matashiya yar Najeriya, ta mutu sakamakon hatsarin mota yan kwanaki bayan ta kammala karatunta a jami'ar tarayya na Otuoke da ke Bayelsa da digiri mafi daraja.
Wani dalibin jami'ar, Jerry Godsent, ne ya sanar da labarin mutuwar Chidera a wata wallafa da ya yi a Facebook a ranar Litinin, 16 ga watan Oktoba.
Chidera ita kadai iyayenta suka haifa
Mutuwar Chidera na zuwa ne kwanaki 12 bayan ta yi bikin kammala karatunta a Facebook. Da yake alhinin mutuwar hazikar matashiyar, Jerry ya bayyana cewa yar jihar Abia ce wacce ta binne mahaifinta da ya rasu a ranar 21 ga watan Satumban 2023.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerry ya ce Chidera ta mutu a ranar 14 ga watan Oktoba kuma ita kadai iyayenta suka haifa. Ya koka cewa yanzu mahaifiyar marigayiyar ta saura ita kadai a duniyar nan. Ya rubuta:
"Ya dade da na ji irin wannan a zuciyata.
"Labari mara dadi:
"Chidera John dita ta inne mahaifinta a ranar 21 ga watan Satumban 2023.
"Ta kammala karau da digiri mafi daraja a ranar 30 ga watan Satumban 2023.
"Ta yi hatsari sannan ta mutu a ranar 14 ga watan Oktoba 2023.
"Marigayiya Midd Chidera Johan daga jihar Abia ta kasance 'ya daya tilo da iyayenta suka haifa.
"Mahaifinki ya tafi kema kin tafi.
"Wa zai kasance tare da mahaifiyarki yanzu.
"Allah ya ji kanki!"
Mercy R Gospel ta ce:
"Wannan ya yi mani ciwo.
"RIP."
Successfully Inemo ta ce:
“Kar A Yi Gaggawan Kiran Jariri Mummuna”: Wata Uwa Ta Girgiza Intanet Bayan Ta Saki Bidiyon Sauyawar Danta
"Na ji babu dadi da jin wannan labarin, Allah ya ji kanki ya Dera."
Sammy Amira ta ce:
"Allah ya ji kanta da rahama."
Jami'ar Gombe ta karrama dattijon da ya kirkiri janareto mara amfani da mai
A wani labari na daban, mun ji cewa jami'ar jihar Gombe ta karrama dan Najeriya mai kirkiran abubuwa, Injiniya Hadi Usman da digirgir a bangaren kimiyya.
A cewar babban mai ba gwamnan jihar Gombe shawara ta musamman kan harkokin labarai, Safianu Danladi Mairiga a dandalin X, an bai wa Usman shaidar digiri a bikin yaye dalibai na jami'ar jihar Gombe da aka kammala kwanan nan.
Asali: Legit.ng