Gwamnatin Borno Ta Haramta Ayyukan Hako Ma'adanai a Fadin Jihar

Gwamnatin Borno Ta Haramta Ayyukan Hako Ma'adanai a Fadin Jihar

  • Gwamnatin Borno karƙashin Gwamna Babagana Zulum ta haramta aikin haƙar ma'adai a faɗin jihar da nufin dawo da zaman lafiya
  • Kwamishinan yaɗa labarai da tsaron cikin gida, Farfesa Usman Tar, ya gargaɗi ma'aikata su kiyaye wannan haramcin ko doka ta hau kansu
  • Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan gwamnatin tarayya ta ce jihohi ba su da ikon tsoma baki a harkokin ma'adanai

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta haramta ayyukan hakar ma'adanai a faɗin sassan jihar da ke Arewa maso Gabas da nufin kawo ƙarshen matsalar tsaro.

Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnatin tarayya ta bakin Ministan ma'adanai, Wale Edum, ta ce jihohi ba su da ikon haramta ayyukan haƙo ma'adanai.

Gwamna Babagana Umar Zulum.
Gwamnatin Zulum ta hana haƙo ma'adanai a jihar Borno Hoto: Professor Babagana Umaru Zulum
Asali: UGC

A ruwayar Premium Times, Ministan ya ce:

"Haramta ayyukan haƙo ma'adanai a faɗin ƙasar nan ba zai yuwu ba a wannan lokacin, kuma batu ne da ya shafi kundin tsarin mulkin ƙasa."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Yayin da Tsohon Minista Kuma Babban Jigon APC Ya Rasu a Arewa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ina amfani da wannan damar na ja hankalin 'yan Najeriya cewa babu wata jiha, ku ji da kyau, babu wata jiha da ke da ikon tsoma baki a harkokin haƙar ma'adanai."

Gwamnatin Borno ta yi fatali da maganar Ministan

Tun ba a je ko ina ba, kwana biyu kacal bayan Ministan ya yi wannan gargaɗi, Gwammatin Borno karƙashin Farfesa Babagana Zulum ta haramta ayyukan a jihar.

Kwamishinan yaɗa labarai da harkokin tsaron cikin gida, Usman Tar, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a 13 ga watan Oktoba, 2023.

Mista Tar, ya gargadi dukkanin ma'aikata a bangaren ma'adinai da su yi biyayya ga haramcin, yana mai gargadin cewa "duk wanda ya yi ƙunnen ƙashi doka zata hu kansa."

“Gwamnatin jiha tana aikin tsara taswira tare da tabbatar da tsare wuraren hakar ma’adanai da nufin tabbatar da doka da oda da kuma tsaron rayukan al'umma.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wani Babban Malami Ya Mutu a Wata Siga Mai Cike da Ruɗani a Jihar Arewa

Mista Tar ya ce nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar za ta fitar da ka'idojin aiki da hanyoyin gudanar da ayyukan haƙar ma'adinai don jagorantar fannin, The Cable ta rahoto.

Shugaba Tinubu Ya Yi Magana Yayin da Tsohon Minista Kuma Babban Jigon APC Ya Rasu a Arewa

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya tura sakon ta'aziyya dangane da rasuwar tsohon minista kuma jigon APC, Sanata Bello Maitama Yusuf.

Shugaban ƙasa ya ce marigayin mutum ne mai garkiya da taimakon matasa kuma 'yan Najeriya ba zasu manta da shi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel