EFCC Ta Kama Wani Mutum Kan Miliyan 57.5 Da Aka Tura Asusun Bakinsa Bisa Kuskure
- Hukumar EFCC ta kama Ibrahim Abubakar, shugaban kamfaninsa kan Naira miliyan 57.5 da aka tura asusun kamfaninsa a Jos, Jihar Filato
- Hukumar yaki da rashawar ta ce Abubakar ya tura miliyan biyar-biyar zuwa asusun ajiyarsa biyu bayan bankin ta sanar da shi cewa bisa kuskure ne aka tura masa
- Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ce an kama Abubakar ne yayin da ya yi yunkurin cire sauran kudin
Filato, Jos - An kama babban manajan kamfanin Shariff Agric and General Service, Ibrahim Abubakar, saboda amfani naira miliyan 57.7 da aka tura asusun kamfaninsa bisa kuskure a Jos, Jihar Filato.
Kakakin Hukumar Yaki da Rashawa EFCC, Dele Oyewale, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 13 ga watan Oktoba, Premium Times ta rahoto.
Oyewale ya ce Baker Drilling Service ta tura miliyan 57.5 zuwa kamfanin Abubakar a maimakon Bluemoe Trade & Service, ya kara da cewa asusun yana bankin United Bank for Africa (UBA) ne.
Ya kara da cewa Abubakar ya tura kudi naira miliyan biyar-biyar zuwa asusunsa na bankin UBA da Keystone.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Kokarin da ya yi na cire sauran kudin ya yi sanadin kama shi."
Oyewale ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.
EFCC Ta Cafke Wani Dattijo a Borno Kan Zargin Handame Dukiyar Magada Har Miliyan 12, Ya Musanta Aikata Laifin
A wani rahoton, Hukumar Yaki da Cin Hanci Da Yi Wa Arzikin Kasa Ta'annati (EFCC) reshen jihar Borno ta kama wani bawan Allah da ake zargi da badakalar makudan kudade har naira miliyan 12.
Wanda ake zargin mai suna Malam Isiyaku Ibrahim, an tuhume shi ne da badakalar kudade tare da gurfanar da shi ne a gaban Usman Fadawu, alkalin babbar kotun jihar Borno.
Yan Sanda Sun Kama Wani Mutum Kan Kange Matarsa Na Tsawon Shekaru Babu Abinci
Yan sanda sun kama magidanci kan zargin kange matarsa na tsawon shekaru ba tare da kulawa ba.
Abdullahi Isa, shine wanda ake zargin ya daure matarsa na tsawon shekaru biyu ba tare da ba ta abinci ba.
Mai rajin kare hakkin dan Adam, Kwamred Lucy Yunana ta kwashi matar zuwa asibiti don duba lafiyarta.
Asali: Legit.ng