'Queen Primer, Royal School Series': Jerin Sunayen Littatafan Da Gwamnatin Kano Ta Haramta

'Queen Primer, Royal School Series': Jerin Sunayen Littatafan Da Gwamnatin Kano Ta Haramta

Saboda rashin jin dadin abubuwan da suke kunshe a ciki, hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta haramta wasu littatafai da ake amfani da su a makarantun reno da firamare.

Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar, Abba Al-Mustapha, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar kwanan nan.

Gwamnatin Kano ta haramta wasu littatafai
Queen Primer, Royal School Series: Jerin Sunayen Littatafan Da Gwamnatin Kano Ta Haramta Hoto: Ajoke Fluency Hub, Kano State Censorship Board
Asali: Facebook

Ya ce hukumar na gudanar da bincike domin daukar mataki a kan wadanda suke da hannu a ciki, yayin da ta haramta amfani da wasu littatafai a jihar Kano a hukumance.

Jerin littatafan da gwamnatin Kano ta haramta

  1. The Queen Primer (dukka wallafar su)
  2. A Royal School Series na kamfanin Nelson Publishers Limited
  3. Basic Science for Junior Secondary School wallafar kamfanin Razat Publishers, wallafar 2018 (JSS3)
  4. Active Basic Science wallafar 2014 na Tola Anjorin, Okechukwu Okolo, Philias Yara, Bamidele Mutiu, Fatima Koki, Lydia Gbagu.
  5. Basic Science and Technology for Junior Secondary Schools 1, 2 and 3: Na W.K Hamzat, S. Bakare.
  6. New Concept English for Senior Secondary Schools for SSS2, Revised edition (wallafar 2018) na J Eyisi, A Adekunle, T Adepolu, F Ademola Adeoye, Q Adams da, J Eto.
  7. Basic Social Studies for Primary Schools na BJ Obebe, DM Mohammed, S N Nwosu, J A Adeyanju da H Carbin.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Jawo Yaron Aminin Buhari, Ya ba Shi Mukami Mai Tsoka a Gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abun da iyaye suka ce game da littatafan da aka haramta

Iyaye sun nuna damuwa sosai game da kasancewar kalaman fasadi a littatafan wanda ke karfafa alakar da masu cutar kanjamau, zubar da ciki, da jima'i da kororon roba.

Kamar yadda jaridar Premium Times ta rahoto, sun yaba ma matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na haramta wadannan littatafai suna masu kira ga sauran gwamnoni da su aikata haka.

Sun nuna damuwa kan tasirin da wadannan littatafai ke da shi a rayuwar yara, suna masu cewa ya kamata a duba manhajar karatu da littatafai don magance matsalar.

Gwamnatin Kano ta kwace littafin ‘Queen Primer’ da wasu masu lalata tarbiya fiye da 1000

A baya mun ji cewa gwamnatin Kano ta kwace kwafin littattafan 'Queen Primer' da ake amfani da su wajen koyar da dalibai a makarantun jihar, rahoton Premium Times.

A ranar Lahadi ne, gwamnatin jihar Kano ta fitar da wata sanarwa inda ta sanar da masu makarantu a jihar aniyarta na haramta amfani da wasu littattafai guda shida a makarantun jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng