Shugaba Tinubu Ya Bukaci Majalisa Ta Amince Da Sabbin Nade-Nade 17

Shugaba Tinubu Ya Bukaci Majalisa Ta Amince Da Sabbin Nade-Nade 17

  • Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya rubutawa majalisar wakilai wasika domin duba yiwuwar tabbatar da sabbin mambobin hukumar NDDC 17
  • Mutum 17 na hukumar NDDC da shugaban ya miƙa wa majalisar, ciki har da shugaban hukumar, Chiedu Ebie, daga jihar Delta
  • Ben Kalu, mataimakin kakakin majalisar, ya karanta wasiƙar shugaba Tinubu a zaman majalisar a ranar Talata

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya nemi majalisar wakilai da ta amince da naɗin shugaban da hukumar raya yankin Neja Delta (NDDC) da mambobin hukumar.

A cewar shugaba Tinubu, bukatarsa ​​ta yi daidai da tanadin sashe na 2(2) na dokar hukumar raya yankin Neja Delta, cewar rahoton jaridar The Nation.

Tinubu ya aike da wasika zuwa ga majalisar wakilai
Shugaba Tinubu ya bukaci majalisar wakilai ta amince da nadin mutum 17 na hukumar NDDC Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Tinubu ya miƙa sunayen mambobin hukumar NDDC 17 zuwa majalisar wakilai

Ben Kalu, mataimakin kakakin majalisar wakilai, ya karanta wasikar shugaban ƙasa a zauren majalisar a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Kara karanta wannan

Tsohon Jigon APC Ya Bukaci a Kori Tinubu Daga Shugabancin ECOWAS, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya miƙa takardar ne ga Tajudeen Abbas, kakakin majalisar wakilai, wacce ke ɗauke da kwanan wata na ranar 30 ga watan Agusta.

Wani ɓangare na wasiƙar na cewa:

"Na yi farin cikin gabatar da sunayen mutum 17 da aka naɗa domin tantancewar ƴan majalisar wakilai a muƙaman shugaba da mambobin kwamitin gudanarwa na hukumar raya yankin Neja-Delta."

Cikakken jerin mambobin hukumar NDDC 17

Ga cikakken jerin sunayen waɗanda aka nada:

1. Mr. Chiedu Ebie – Shugaba daga jihar Delta

2. Dr. Samuel Ogbuku – Manajan darakta daga jihar Bayelsa

3. Mr. Boma Iyaye – Babban daraktan harkokin kuɗi daga jihar Rivers

4. Mr. Victor Antai – Babban daraktan aikace-aikace daga jihar Akwa-Ibom

5. Ifedayo Abegunde – Babban daraktan gudanarwa daga jihar Ondo

6. Sanata Dimaro Denyanbofa daga Bayelsa

7. Mista Abasi Ndikan Nkono daga jihar Akwa Ibom

Kara karanta wannan

Atiku Ya Shigar Da Sabbin Shaidun Amfani Da Takardun Bogi Kan Shugaba Tinubu, Bayanai Sun Bayyana

8. Honarabul Monday Igbuya daga Delta,

9. Tony Okocha daga Rivers

10. Honarabul Patrick Aisowieren daga Edo

11. Mista Kyrian Uchegbu daga jihar Imo

12. Victor Kolade Akinjo daga Ondo

13. Dimgba Eruba daga Abia,

14. Mr. Asu Oku Okang daga Cross River,

15. Honarabul Nick Wende - wakilin Arewa ta Tsakiya,

16. Honarabul Namdas Abdulrazak - wakilinin Arewa maso Gabas, da kuma

17. Dakta Ibrahim Abdullahi Gobir – wakilin Arewa maso Yamma

An Bukaci ECOWAS Ta Kori Tinubu

A wani labarin kuma, tsohon jigo a jam'iyyar APC, Timi Frank ya buƙaci ƙungiyar rsya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) ta ƙwace shugabancinta a hannun Shugaba Tinubu.

Timi ya bayyana cewa cigaba da zaman Tinubu a matsayin shugaban ƙungiyar zai sanya ƙimarta ta zube.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng