Bidiyon Yan Mata 10 a Kan Babura Ya Haddasa Cece-Kuce, Sun Jeru Sanye Da Anko

Bidiyon Yan Mata 10 a Kan Babura Ya Haddasa Cece-Kuce, Sun Jeru Sanye Da Anko

  • Akalla mata 12 ne aka gano jere reras a kan babura a cikin wani bidiyo da ya dauka hankali a soshiyal midiya
  • Matan da ke sanye da anko na leshi da gwaggwaro sun tashi kan mutane yayin da suka mamaye wani waje cikin annashuwa da walwala
  • Yayin da mutane da dama suka yaba kyawun da suka yi, wasu sun cika da mamakin dalilin da zai sa mata su tuka babura

Jama'a sun yi cece-kuce yayin da wani bidiyo da ke nuna wasu yan mata suna tuka babura cike da farin ciki ya yadu a soshiyal midiya.

Daya daga cikin yan matan, @user1868198263041, ta yada hadadden bidiyon a dandalin sada zumunta na TikTok.

Yan mata jere a kan babura
Bidiyon Yan Mata 10 a Kan Babura Ya Haddasa Cece-Kuce, Sun Jeru Sanye Da Anko Hoto: @user1868198263041
Asali: TikTok

A cikin bidiyon, yan matan sun kasance sanye da anko na leshi da gwaggwaro yayin da suke hanyarsu ta zuwa wani taro cikin salo.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Yayin Da Yan Gidan Magajiya Suka Bazama Neman Kwastamomi a Kasuwar Legas

Da isarsu wajen, sai yan matan suka fara magana ta hanyar daga murya da yarensu cikin yanayin da ke nuna suna cikin tsananin farin ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama sun ji sha'awar yanayinsu da yadda suka tafiyar da harkokinsu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Gr8rNigeria ya ce:

"Ina zuba ido don ganin yan Najeriya sun yi nasu a kan kekuna.
"Ya kamata a cire matsin nan na son zama "masu mota"; matsin lambar da ya haifar da tarin rashawa a kasarmu.
"Muna bukatar daraja mutunci a kan mallakar kayan alatu.
"Mallakar kyawawan dabi'u shi ya fi."

@Faithysia_blunt ta ce:

"Wannan yana da kyan kallo, me yasa mutane ke yi masu dariya? Shin kun fi son masu fitowa daga motar Benz wanda mazajen wasu suka siya masu?"

@the_jerrymanuel ta ce:

Kara karanta wannan

Wani Mutum Ya Baje Kolin Gidan Da Yake Haya, Bidiyon Ya Girgiza Intanet

"Amma magana ta gaskiya a matsayin matashiyar budurwa me zai sa kuma ta yaya kike iya tuka babur?"

@OlaSupercc ta ce:

"Menene wannan, Menene wannan!! Menene wannan....sautin da ke tashi a kaina yanzu haka."

Yadda yan gidan magajiya suka mamaye kasuwa a Legas don neman kwastamomi

A wani labari na daban, mun ji cewa a yanzu yan gidan magajiya basa tsayuwa a bakin hanya kamar yadda suka saba da daddare, maimakon haka, sun koma yin dafifi a kasuwar Lagas suna neman abokan ciniki.

Wani shararren wajen siye da siyarwa na Ikeja (ICM) ya zama dandalinsu, inda yan mata da ke ganiyar shekaru 20 da 30 suke fakewa a wajen sanye da dangalallun kayansu suna neman maza da za su kwashe su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng