Gwamnatin Kano Ta Kwace Littafin ‘Queen Primer’ Da Wasu Masu Lalata Tarbiya Fiye Da 1000
- Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano tana ci gaba da tabbatar da hukuncin gwamnatin jihar na haramta amfani da wasu littattafai a makarantun jihar
- Abba Al-Mustapha, shugaban hukumar tace fina-fina na Kano, ya jagoranci kwace kwai-kwafin littafin 'Queen Premier' da wasu masu alaka a jihar
- Gwamnatin Kano dai ta ce akwai fasadi a cikin littafin wanda bai kamata yara su ji ko su koye su ba
Jihar Kano - Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta kwace kwafin littattafan 'Queen Primer' da ake amfani da su wajen koyar da dalibai a makarantun jihar, rahoton Premium Times.
A ranar Lahadi ne, gwamnatin jihar Kano ta fitar da wata sanarwa inda ta sanar da masu makarantu a jihar aniyarta na haramta amfani da wasu littattafai guda shida a makarantun jihar.
Kano: Abba Gida Gida Ya Amince Da Biyan Makudan Kudade Ga Daliban Da Ke Jami'o'in Najeriya, Ya Bayyana Dalili
Mun kwace littattafan Quen Premier 1,200, Hukumar tace fina-finai na Kano
Shugaban Hukumar tace fina-finan, Abba Al-Mustapha, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Godiya ta tabbata ga Allah, kowa a Kano ya san cewa mun wayi gari da wata barazana a kan wani littafi, wanda ake amfani da shi wajen koyar da yaranmu a makarantu mai suna 'Queen Primer'."
“Littafin yana cike da maganganu na fasadi wadanda ba su kamata a ce ’ya’yanmu sun ji su ba ko kuma an karantar da su ba.
"Na tattara tawagata don shiga aiki, kuma zuwa yanzu sun kwace kwafi-kwafi na littattafan guda 1,200 daga shagunan siyar da takardu da kasuwanni. Ba za mu yi kasa a gwiwa ba a bincikenmu na gano tushen abun don ganin wadanda ke da hannu a ciki sun fuskanci doka.
"Matsayin hukumar tace fina-finai ta jihar Kano shine cewa dole mu haramta amfani da siyar da wannan littafi da littattafai masu alaka a jihar Kano. Mun kum haramta amfani da su don koyarwa a dukkan makarantun firamari da ke jihar."
Kungiyar MURIC ta yabawa Abba Kabir Yusuf kan haramta amfani da wasu littattafai a makarantu
A gefe guda, mun ji cewa Kungiyar Kare Hakkin Musulmai (MURIC) ta yaba wa Gwamna Abba Kabir na haramta amfani da wasu littattafai a makarantun Nursery da firamare a jihar.
Shugaban kungiyar a jihar, Hassan Indabawa shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Juma'a 6 ga watan Oktoba.
Asali: Legit.ng