Ana Tsammanin Haihuwan Yara 365,593 a Jigawa a 2023

Ana Tsammanin Haihuwan Yara 365,593 a Jigawa a 2023

  • Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce an haifi jarirai sama da dubu 200 daga cikin sama da dubu 300 da ake tsammani a wannan shekarar ta 2023
  • Kwamishinan lafiya a jihar ya ce gwamnati a shirye take don fito da hanyoyin tsarin iyali a saukake kuma na zamani
  • Kwamishinan ya ce an samar da sabon sashe na kula da tsarin iyali saboda irin muhimmancin da gwamnati ta bawa fannin

Jihar Jigawa - Gwamnatin Jihar Jigawa ta ce tana tsammanin za a haifi jarirai 365,595 a jihar a shekarar 2023.

Kwamishinan lafiya na jihar, Abdullahi Kainuwa, shi ne ya bayyana haka a bikin ranar maganin kayyade iyali da aka gudanar a Dutse, babban birnin jihar, ranar Alhamis.

Yayin taron, Kainuwa ya ce mata da suka isa haihuwa na karbar magungunan hana haihuwa a cibiyoyin kiwon lafiya akalla 300 daga cikin 761 da ake da su a fadin jihar, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Ahaf: Bayan kashe N-Power, Tinubu ya fadi yadda zai sharewa matasa hawaye a Najeriya

Ya ce an haifi jarirai 273,000 daga cikin 365,595 a rahoton watan Yuni.

"Muna tsammanin za a haifi jarirai 365,595 wannan shekarar, tuni adadin ya haura 273,000 zuwa watan Yuni, sauran wanda za a haife ba su wuce 1000 ba," in ji Kainuwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kainuwa ya ce jihar na da mata da suka isa haihuwa 1,608,616 kuma ma'aikatar lafiya na da kudirin cewa zuwa 2027, kaso 30 na matan Jigawa na amfani da hanyoyin takaita haihuwa na zamani.

"Taro ne don wayar da kai kan muhimmanci, da kuma fito da hanyoyin kayyade iyali don inganta lafiya da walwalar al'umma.
"Amfani da hanyoyin kayyade iyali zai taimaka wajen bada tazarar haihuwa, inganta lafiyar uwa da jariri, da kuma taimaka haɓakar tattalin arziki," in ji Kainuwa.

An tattara alkaluman ne daga cibiyoyin kiwon lafiya da ake shigarwa yayin duba lafiya kafin daukar ciki, daukar ciki, da kuma bayan haihuwa. Za a iya cewa, da yawa daga cikin mata basa zuwa asibiti don duba lafiyarsu akan abin da ya shafi ciki.

Kara karanta wannan

Sabon Rusau: Za a Rushe Wasu Fitattun Kasuwanni 3 a Najeriya, Bayanai Sun Fito

A Jigawa, adadin wanda ke haihuwa a asibiti ya karu daga kaso 6.8 zuwa 18.2 a shekarar 2023 sannan amfani da maganin takaita haihuwa ya karo daga sama da kaso daya a 2015 zuwa kaso 3.5 a 2023, a rahoton binciken MICS da aka sabunta a 2021.

Kasafin da aka warewa tsarin iyali

Sannan, Premium Times ta ruwaito ma'aikatar lafiya tsakanin 2020 - 2023 ta fitar da kudade kashi-kashi don taimakawa tazarar haihuwa a jihar.

A 2020, jihar ta yi kasafin naira miliyan 10 don tsarin iyali, sai dai ba a fitar da kudin ba. A 2021 an ware naira miliyan 20, sai dai iya N7,628,000 aka fitar don tsarin iyali.

A shekarar 2022, an ware makudan kudade wajen taimakawa tazarar haihuwa inda aka fitar da naira miliyan 30, an bayar da naira miliyan 23 a wannan shekarar, a 2023, naira miliyan 35 aka ware, amma har zuwa Oktoba, ba a saki kudi don tsarin iyali a jihar ba.

Kara karanta wannan

Subhanallahi: Gobara Ta Kone Mutum 6 Kurmus a Kano, Bayanai Sun Fito

Da yake martani game da yadda kasafin ya kasance, Kainuwa, ya ce ya fara aiki wata daya da ya wuce kuma yayi alƙawarin gyara duk wata matsala, ya ce a shirye yake don ganin al'umma ta amfana cikin sauki.

"An kirkiri sabon sashe don tsarin iyali don nuna irin muhimmanci da jihar ta bawa fannin don saukaka hanyoyin kayyade iyali a zamanance da saukake ga duk mata masu sha'awar haka," in ji Kainuwa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164