Yan Bindiga Sun Halaka Mutum 4 a Wani Sabon Hari a Jihar Kaduna
- Ƴan bindiga sun kai wani sabon hari a unguwar Dandali cikin ƙaramar hukumar Zariya a jihar Kaduna
- Miyagun ƴan bindigan sun halaka mutum huɗu tare da sace wasu mutum biyr a yayin harin da suka kai
- Jami'an tsaro sun kawo agajin gaggawa inda suka fatattaki ƴan bindigan d asuka kawo mummunan harin
Jihar Kaduna - Wasu ƴan bindiga sun kai farmaki a Unguwar Dandali da ke ƙaramar hukumar Zariya a jihar Kaduna inda suka kashe mutum huɗu tare da raunata wasu mutum biyar.
Da yake tabbatar da aukuwar lamarin hakimin yankin, Malam Sunusi Yusuf ya bayyana cewa ƴan bindigar sun isa ne da misalin karfe 10:30 na daren ranar Juma'a, 6 ga watan Oktoba, inda suka fara harbe-harbe a iska, cewar rahoton Daily Trust.
Ya bayyana cewa ƴan bindigan sun yi nasarar harbin mutum 9 tare da yin awon gaba da mutane 5 kafin isowar jami’an tsaro inda suka yi artabu da su.
"A cikin mutum tara da aka harba, mutum huɗu nan take suka mutu yayin da mutum biyar suka samu munanan raunuka."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Saboda karfin da jami’an tsaro ke da shi, ƴan bindigan sun koma daji bayan harbe wadanda suka mutu tare da yin awon gaba da wasu mutane huɗu."
Mutanen da ƴan bindigan suka halaka sun haɗa da, Dahiru Tsalha Wawo, Bashir Salisu, Umar Yahuza da Umar Bako.
Yayin da wadanda suka samu raunuka daban-daban kuma aka kwantar da su a asibiti sun hada da, Abubakar Yahuza, Bala Shamaki, Aliyu Ahmed, da Abdullahi Mamuda.
Ƴan sakai sun ƙwato mutanen da aka sace
Ƴan sakai a unguwar Jaji da ke a ƙaramar hukumar Igabi sun tare ƴan bindigan, inda suka ƙwato mutanen da suka sace a safiyar ranar Asabar, 7 ga watan Oktoba, kuma har an sada su da iyalansu.
An gudanar da Sallar jana'izar mutane huɗu da suka rasa rayukansu daga bisani aka binne su a maƙabartar Unguwar Dankali a Hayin Dogo kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Dalilin Sace Daliban FUDMA
A wani labarin kuma, mataimakin shugaban jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma (FUDMA), ya bayyana dalilin da ya sanya ƴan bindiga suka sace ɗalibai a jami'ar.
Farfesa Armaya'u Bichi ya bayyana cewa ƴan bindigan ramuwar gayya suka yi kan harin da jami'an tsaro suka kai kan ƴan uwansu.
Asali: Legit.ng