Ministan Tinubu Ya Suma a Majalisa Yayin Da Wani Dan Jarida Ya Rasu

Ministan Tinubu Ya Suma a Majalisa Yayin Da Wani Dan Jarida Ya Rasu

  • Abbas Balarabe, wanda Shugaba Tinubu ya naɗa a matsayin minista, ya jefa majalisar datawa cikin fargaba bayan ya suma a yayin da ake tantance shi
  • Ba tare ɓa bata lokaci ba likitocin majalisar suka yi kan Balarabe, yayin da shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya dakatar da masu ɗaukar hoto da bidiyo
  • A wani lamari makamancin haka, Tijani Adeyemi, wakilin jaridar Tribune a majalisar, ya rasu sakamakon bugun zuciya

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ta shiga cikin ruɗani da tashin hankali a ranar Laraba, 4 ga watan Oktoba, lokacin da ministan da Bola Tinubu ya naɗa, Abbas Balarabe, ya faɗi kuma ya suma a yayin da ake tantance shi a zauren majalisar.

Shugaba Tinubu ya miƙa sunan Balarabe ga majalisar dattawa domin tantancewa tare da tabbatar da shi a matsayin minista mai wakiltar jihar Kaduna kuma a matsayin wanda zai maye gurbin Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

"Abin Da Ya Sumar Dani A Wurin Tantancewa", Minista Ya Yi Bayani Bayan Faduwa A Majalisa

Abbas Balarabe ya suma a majalisa
Bayan Abbas Balarabe ya samu, wani dan jarida ya rasu a majalisar dattawa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

Yadda Balarabe ya suma yayin tantance ministoci a majalisa

Jaridar The Punch ta ce kusan mintuna 15 da fara tantance shi, Balarabe ya suma a tsaye lokacin da yake a kan mumbarin majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga nan sai Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattiwan ya yi umarnin cewa a ba shi sukari da ruwa sannan ya umarci ƴan jarida da masu daukar hoto da su dakatar da ɗaukar abin da ke faruwa.

A lokaci guda kuma, likitoci sun halarci wurinsa tare da ba shi taimakon farko na gaggawa.

Bayan haka, Yemi Adaramodu, kakakin majalisar dattawa, ya shaida wa manema labarai cewa, majalisar ta tabbatar da Balarabe a matsayin minista saboda ya tsallake duk wasu abubuwan da majalisar ta tambaye shi.

Cikakkun bayanai na ɗan jaridan da ya rasu a majalisar dattawa

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Bayyana Halin Da Wakilin Jihar Kaduna Yake Ciki Bayan Ya Kife a Wajen Tantance Ministoci

A wani lamari makamancin haka, wani ɗan jarida da ke aiki da jaridar Tribune a majalisar dattawa, Tijani Adeyemi, ya mutu sakamakon bugun zuciya a ɗaya daga cikin motocin majalisar.

Adeyemi ya hau ɗaya daga cikin motocin ne daga babbar ƙofar Mopol da misalin ƙarfe 10 na safe.

Lokacin da ya isa wurin bincike, an gano cewa ba ya numfashi. Ƙoƙarin farfado da shi ya ci tura, kuma an tabbatar da mutuwarsa bayan an garzaya da shi asibiti.

Balarabe Ya Magantu Kan Abin Da Ya Sumar Da Shi

A wani labarin kuma, Abbas Balarabe ya bayyana dalilin da ya sanya ya suma lokacin da ake tantance shi a majalisar dattawa.

Balarabe ya yi bayanin cewa tsabagen gajiyar da ta yi masa katutu ce ta sanya ya kife a majalisar ana tsaka da tantance shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng