Tsautsayi Ya Sanya Motar Malamin Makaranta Ta Yi Sanadin Mutuwar Daliba a Legas

Tsautsayi Ya Sanya Motar Malamin Makaranta Ta Yi Sanadin Mutuwar Daliba a Legas

  • Wata ɗaliba a jihar Legas ta gamu da ajalinta bayan motar wani malamin makarantarsu ta tunkuɗe ta
  • Ɗalibar dai na tsaka da yin wasa da ƙawayenta ne lokacin da motar da aka ajiye ta taho da baya-baya ta tunkuɗe ta
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce an tsare malamin domin gudanar da bincike

Jihar Legas - Wata daliba ƴar shekara 10 mai suna Rofiat ta rasa ranta bayan da wata mota ta tunkuɗe ta a harabar makarantarsu mai suna Isiu Grammar School da ke unguwar Ikorodu a jihar Legas.

Jaridar The Punch ta kawo rahoto a ranar Laraba cewa lamarin ya auku ne a ranar Juma'a, 29 ga watan Satumba.

Motar malamin makaranta ta yi ajalin daliba a Legas
Dalibar ta rasu bayan da motar malamin ta tunkude ta Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yadda lamarin ya auku

Rahotanni sun ce Rofiat ta haɗu da ƙawayenta a filin wasan makarantar a lokacin da suke shirin tashi. Bayan wani lokaci, wata mota da wani malami mai suna Dele ya ajiye a kusa da wajen sai ta fara yin baya har zuwa inda take.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Babban Kusan Gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɗalibar wacce ba ta lura da abin da ke faruwa ba, kawai sai motar ƙirar Nissan ta tunkuɗe ta, rahoton The Star ya tabbatar.

Wani mazaunin unguwar ya bayyana cewa:

"An shaida mana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na rana. Tun safe aka ajiye motar a wajen bayan malamin ya iso. Ba mu san yadda motar ta matsa daga inda aka ajiye ta ba."
"Rofiat tana bayan motar ne. A lokacin da motar ta buge ta, ƙarfin bugun ya sanya goshinta ya bugi ƙasa. Wasu ɗalibai ne suka yi gaggawar kiran malaman da suka zo wurin, suka tarar ta daina motsi."
"Bayan rasuwarta, wasu jami’an ƴan sanda sun zo harabar makarantar domin ɗaukar hotuna tare da yi wa wasu malaman da ke bakin aiki tambayoyi a lokacin da lamarin da ya auku."

Kara karanta wannan

Babban Sanata Da Iyalansa Sun Mutu a Wani Mummunan Hatsarin Jirgin Sama, Bayanai Sun Fito

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da aukuwar lamarin.

"Eh, tabbas lamarin ya auku. Ana tsare da mamallakin motar. Ana cigaba da gudanar da bincike." A cewarsa.

Hatsarin Mota Ya Ritsa Da Bayin Allah

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da mutane masu yawa akan titin hanyar Legas-Ibadan.

Hatsarin motar wanda ya ritsa da mutum 16, ya yi sanadiyyar rasuwar mutum ɗaya inda wasu mutum bakwai suka samu raunika.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng