Kogi: Gwamna Yahaya Bello Ya Nada Sabbin Hadimai 215

Kogi: Gwamna Yahaya Bello Ya Nada Sabbin Hadimai 215

  • Gwamnan jihar Kogi ya yi ƙarin masu taimaka masa domin tafiyar da harkokin gwamnati a jihar
  • Gwamna Yshaya Bello ya naɗa sabbin masu ba shi shawara na musamman da mataimaka na musamman har mutum 215
  • Sakatariyar gwamnatin jihar ita ce ta sanar da naɗin sabbin hadiman, inda ta ce naɗinsu zai fara aiki ne daga ranar 29 ga watan Satumba

Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya yi naɗin sabbin mataimaka guda 215 a gwamnatinsa.

Naɗin sabbin hadiman na gwamnan na zuwa ne yayin da wa'adinsa, yake sauran ƴan watanni kaɗan ya zo ƙarshe.

Gwamna Yahaya Bello ya nada sabbin hadimai
Nadin sabbin hadiman na zuwa ne wa'adin gwamnan na dab da kare wa Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Jaridar Tribune ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga hannun sakatariyar gwamnatin jihar, Dr. Folashade Ayoade.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Abba Gida-Gida Ya Naɗa Sabbin Shugabanni 10 a Hukumomin Gwamnatin Kano

Sabbin hadiman sun ƙunshi mutane daga dukkanin ƙananan hukumomi 21 da ke cikin jihar Kogi, kuma naɗinsu ya fara aiki daga ranar 29 ga Satumban 2023, rahoton Kogi Reports ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Waɗanne muƙamai aka ba su?

Bisa ga bayanin da aka bayar a cikin sanarwar, nadin ya haɗa da mutum 26 da aka naɗa a matsayin masu ba gwamna shawara na musamman, mutum 128 da aka naɗa manyan mataimaka na musamman, da ƙarin wasu mutum 51 da za su kasance mataimaka na musamman da dai sauransu.

Wasu daga cikin sabbin masu ba da shawara na musamman da aka nafa sun haɗa da James Modu Kaura (cigaban ƙarafa), Siaka Ibrahim (ƴan asalin jihar Kogi a ƙasashen waje), Nusa Yahaya (harkokin ƙananan hukumomi na ƙaramar hukumar Igbalamela/Odolu).

Abduluhai Yunusa (harkokin ƙananan hukumomi na ƙaramar hukumar Ofu), James Babatunde (Makamashi), Odoh Akowe (Ilimin Siyasa), Umar Isah Edibo (Jagoranci), Oluwakayode Emmanuel (Ilimantar da yara mata) da Onu Salifu (bunƙasa al'adu).

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari a Jihar Arewa, Sun Halaka Babban Kusan Gwamnati

Sauran sun haɗa da Mohammed Attai Yusuf, babban mataimaki na musamman kan samar da ayyukan yi (Kogi ta Gabas), Nuhu Isa Alifia (cigaban al'umma II), Mumin Suleiman Ahmed (gyaran Hanya) da Siaka Alih (gudanar da masana'antu), da sauransu.

Gwamna Abba Ya Yi Sabbin Nade-Nade

A wani labarin kuma gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa sabbin shugabannin wasu ma'aikatu da hukumomin gwamnatin jihar.

Gwamnan wanda ya naɗa shugabannin ma'aikatu 10, ya buƙaci waɗanda aka naɗa da su yi amfani da kwarewarsu wajen gudanar da ayyukansu ta yadda za su yi wa al’ummar jihar hidima da kuma sauke nauyin da aka ɗora musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng