Tallafin Man Fetur: SERAP Ta Maka Gwamnonin Najeriya 36 Kara a Gaban Kotu

Tallafin Man Fetur: SERAP Ta Maka Gwamnonin Najeriya 36 Kara a Gaban Kotu

  • Ƙungiyar SERAP ta maka gwamnonin Najeriya 36 ƙara a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Legas
  • Ƙungiyar ta maka gwamnonin ƙarar ne kan kudaɗen tallafin N72bn da suka karɓa daga gwamnatin tarayya
  • Ƙungiyar na neman kotun ta tilasta gwamnonin bayyana yadda suka kashe kuɗaɗen da kuma waɗanda suka amfana da su

Jihar Legas - An gurfanar da ɗaukacin gwamnonin jihohin Najeriya 36 a gaban kotu, sakamakon gazawar su na bayar da bayanai kan tallafin N72bn da gwamnatin tarayya ta ba su zuwa yanzu domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur a kasar.

A cewar ƙungiyar SERAP wacce ta shigar da ƙarar, gwamnonin jihohin sun gaza yin lissafin kashe kuɗaɗen tallafin da suka karɓa daga gwamnatin tarayya na N72bn, ciki har da cikakkun bayanai na wadanda suka ci gajiyar tallafin da kuma tallafin da aka samar da kuɗaɗen.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC Ya Yi Kalamai Masu Ratsa Zuciya Bayan Kotu Ta Tabbatar Da Nasararsa a Zabe

SERAP ta maka gwamnoni kara a kotu
SERAP ta maka gwamnonin Najeriya 36 kara a gaban kotu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

A baya-bayan nan ne dai gwamnatin tarayya ta raba N2bn daga cikin kuɗaɗen tallafi na N5bn ga kowace jiha da kuma babban birnin tarayya Abuja, domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur.

Wane buƙatu SERAP ke nema a kotun?

A cikin ƙarar mai lamba FHC/L/CS/1943/2023 da aka shigar a ranar Juma'a a babbar kotun tarayya da ke Legas, SERAP na neman:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Kotun ta tilasta wa kowane daga cikin gwamnonin jihohi 36 da su yi lissafin yadda suka kashe N2bn na kuɗaɗen tallafin da suka karɓa daga gwamnatin tarayya."
"Kotun ta umarci tare da tilasta kowane daga cikin gwamnonin jihohi 36 da ya bayyana cikakkun bayanai na waɗanda suka ci gajiyar tallafin da kuma tallafin da aka ba wa ƴan Najeriya talakawa da marasa galihu da kuɗaɗen."
"Kotun ta umarci tare da tilasta kowane daga cikin gwamnonin jihohi 36 su umarci hukumomin yaƙi da cin hanci na ICPC da EFCC su sanya ido kan yadda ake kashe kuɗaɗen tallafin."

Kara karanta wannan

Rikici Kan Budurwa Ya Sanya Wani Dalibi Ya Rasa Ransa a Wata Babbar Jami'a a Arewacin Najeriya

Lauyoyin SERAP, Kolawole Oluwadare da Blessing Ogwuche ne suka shigar da ƙarar a madadin ƙungiyar.

Gwamnan Sokoto Ya Yaba Da Hukuncin Kotu

A wani labarin kuma, gwamnan jihar Sokoto ya yaba da hukuncin da kotun zaɓe ta yanke wanda ya tabbatar da nasararsa a zaɓen 2023.

Gwamna Ahmed Aliyu ya bayyana cewa hukuncin kotun ya nuna cewa ɓangaren shari'a ba ya nuna son rai a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng