An Cafke Dalibai 6 Na Jami'ar FUDMA Bisa Zargon Halaka Abokinsu Kan Wata Budurwa

An Cafke Dalibai 6 Na Jami'ar FUDMA Bisa Zargon Halaka Abokinsu Kan Wata Budurwa

  • Wani ɗalibin jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma (FUDMA) a jihar Katsina, ya rasa ransa kan rigima saboda budurwa
  • Rundunar ƴan sandan jihar ta cafke ɗalibai shida wanda ake zargin suna da hannu a rasuwar ɗalibin
  • Rundunar ta bayyana cewa za ta gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar abin da ya faru

Jihar Katsina - An cafke wasu ɗalibai shida na jami'ar gwamnatin tarayya da ke Dutsinma (FUDMA), a jihar Katsina bisa zargin kashe abokin karatunsu, Abubakar Nasir-Barda, ɗalibi mai shekara 21 wanda yake a 200L, kan wata budurwa wacce ƴar makarantar ce.

Mummunan lamarin wanda ya shafi daliban jami'ar takwas, an ce ya faru ne a unguwar Darawa da ke ƙaramar hukumar Dutsinma a jihar Katsina a ranar Alhamis da misalin karfe 1:20 na rana, cewar rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali Bayan Yan Bindiga Sun Kona Gidan Babban Dan Majalisa a Najeriya

Wani dalibi ya rasu a jami'ar FUDMA
Yan sanda sun cafke dalibai shida kan aukuwar lamarin Hoto: Federal University, Dutsinma
Asali: Facebook

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 30 ga watan Satumba, ya ce lamarin ya faru ne sakamakon zazzafar gardama a tsakanin ɗaliban, wacce ta rikiɗe zuwa faɗa har ta yi sanadiyar mutuwar ɗaya daga cikin ɗaliban.

Sanarwar ta ce rundunar ta ɗauki lamarin da muhimmanci kuma tana gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar lamarin, rahoton Channels tv ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ƙara da cewa an kama shida daga cikin ɗaliban da ke da alaka da lamarin.

Rundunar ta kuma bayyana cewa tana aiki tuƙuru domin tattara da kuma nazarin dukkanin shaidun da ake da su, ciki har da shaidun gani da ido, domin gano abubuwan da suka faru dangane da lamarin.

Ya kuma musanta ikirarin da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta na yanar gizo cewa mumunan mutuwar dalibar ta faru ne saboda "matsalar addini" inda ya buƙaci jama'a da su yi watsi da duk wata jita-jita da ake yaɗawa.

Kara karanta wannan

An Tsaurara Matakan Tsaro Yayin Da Gwamnan APC Ke Shirin Tantance Makomarsa a Kotun Zaɓe

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"Yayin da ake cigaba da gudanar da bincike, za a riƙa bayyana ƙarin bayani ga jama'a jama'a domin tabbatar da gaskiya."

Yan Sanda Sun Cafke Masu Garkuwa Da Mutane

A wani labarin kuma, rundunar ƴan sandan jihar Benue ta cafke wasu miyagu da ake zargi da aikata laifin garkuwa da mutane.

Jami'an ƴan sandan rundunar sun kuma kuɓutar da wasu mutum shida da miyaguj suka yi garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel