Abinda Ya Jawo Hatsarin Jirgin Ruwa Har Sau Uku a Mako 1,Gwamnatin Adamawa
- Muhimman dalilan da suka haddasa hatsarin jirgin ruwa sau uku cikin mako ɗaya a jihar Adamawa sun bayyana
- Gwamnatin Ahmadu Fintiri ta bayyana cewa zata ɗauki matakai da tabbatar da dokokin ruwa domin kare aukuwar haka a gaba
- Mutane da yawa ne suka rasa rayukansu sanadiyyar haɗurran jiragen ruwa uku a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya
Adamawa - Gwamnatin jihar Adamawa ta gano abubuwan da suka haddasa hatsarin kwale-kwale guda uku a jihar cikin mako guda.
Hatsarin ruwa ya yi ajalin mutane da dama a cikin kwanaki takwas da suka gabata, lamarin da ya janyo suka kan yadda ake tafiyar da harkokin sufurin ruwa a jihar da ke Arewa maso Gabas.
Na baya bayan nan ya auku ne a ranar Litinin 11 ga watan Satumba, inda wani Kwale-kwale ya nutse da mutane a yankin karamar hukumar Mayobelwa, mutum 2 suka mutu.
Kwana huɗu kafin haka, Wani jirgin ruwa da ya ɗauki fasinjoji 23 da suka ƙunshi manoma da 'yan kasuwa daga ƙauyen Rugange zuwa garin Yola ya nutse a tafkin Najwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Haɗarin wanda ya auku a kusa da kauyen Dandu a tafkin Najwa ya laƙume rayukan mutane 15, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Yayin da ake kokarin lalubo mutanen da suka ɓata a tafkin Najwa ranar Litinin, aka sake samun labarin wani Jirgin ruwa da ya ɗauko mutane da yawa ya kife a Gurin, ƙaramar hukumar Fufore.
Mennene ya haddasa waɗan nan haɗurran a Adamawa?
Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Adamawa, Muhammad Amin Sulaiman, ranar Talata ya bayyana abubuwan da gwamnati ta gano suka haddasa haɗurran.
Ya bayyana lodi fiye da ƙima, rashin kula da yanayi, da kuma rashin amfani da rigar ruwa a matsayin manyan dalilin da ke haddasa hatsarin, Trust Radio ta rahoto.
Ya ƙara da cewa gwamnatin jihar karkashin gwamna Ahmadu Fintiri na aiki tuƙuru domin daukar matakan tsare lafiya da kare aukuwar irin haka nan gaba.
Gwamna Fintiri, wanda ya kai ziyarar jaje garin Gurin ranar Talata ya ce ya umurci dukkanin hukumomin da abin ya shafa su tabbatar ana bin matakai da suka hada da hana lodi fiye da kima da kuma amfani da rigar ruwa.
Tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi Ya Fice Daga PDP Zuwa APC a Abuja
A wani labarin kuma Yayin da ake tunkarar zaben gwamnan jihar Kogi, jam'iyyar APC ta yi babban kamu daga babbar jam'iyyar adawa PDP.
Tsohon mataimakin gwamnan jihar, Arc Yomi Awoniyi, ya shiga jam'iyyar APC a hukumance ranar Talata a hedkwata da ke Abuja.
Asali: Legit.ng