Kwararren Akanta, Akintola Williams, Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Masanin harkokin da suka shafi Akanta, Akintola Williams, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 104 a duniya
- Marigayin, wanda shi ne ɗan Najeriya na farko da ya zama kwararren Akanta na duniya, ya mutu wata ɗaya bayan bikin kara shekararsa
- Yana ɗaya daga cikin waɗanda suka jagoranci kafa kungiyar ICAN a Najeriya kuma ya ba da gudummuwar mai tarin yawa a lokacin rayuwarsa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Masani kuma kwararren a fannin da ya shafi lissafin kuɗi watau Akanta, Pa Akintola Williams, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 104 a duniya.
Channels tv ta ruwaito cewa mamacin, wanda ake kira da, "Doyen na Akanta" ya mutu ne wata ɗaya da 'yan kwanaki bayan ya yi murnar ƙarin shekara.
Bayanai sun nuna cewa Marigayin ya yi bikin zagayowar ranar haihuwarsa na cika shekaru 104 a duniya ranar 9 ga watan Agusta, 2023.
Pa Williams, shi ne ɗan Najeriya na farko da ya cancanta kuma ya zama mamban ƙungiyar Akantoci a wasu ƙasashen duniya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Taƙaitaccen tarihin marigayi Williams
Daily Trust ta tattaro cewa mamacin shi ne mutum na farko daga ƙasashen yankin sahara a nahiyar Afirka da ya zama kwararren masanin harkokin kuɗi (Chatered Accountant).
Ya samu nasarar kafa wannan tarihi ne bayan ya ci jarabawar tantancewa a makarantar "Chartered Accountants of England and Wales (ICAEW)" a shekarar 1949.
Masanin ya taka rawa gagara misali wajen bunkasa karatun Akanta a ƙasar nan ta hanyar kafa ƙungiyar Akanta ta Najeriya, wacce daga bisani aka sauya sunan ta koma Institute of Chartered Accountants of Nigeria (ICAN).
Yana ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa kungiyar ICAN sannan kuma ya taka rawa wajen kafa kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Najeriya, wacce yanzu ake kira Nigerian Exchange Group.
Kafin rasuwarsa, Williams ya samu kyautuka da yawa da suka hada da Order of the Federal Republic (OFR) da kuma Nigerian National Order of Merit (NNOM).
Mutane 15 Sun Mutu Yayin da Jirgin Ruwa Ya Nutse a Jihar Adamawa
Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane 15 suka mutu yayin da wani jirgin ruwa da ya ɗauko Fasinjoji harda kananan yara ya yi hatsari a jihar Adamawa.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar ya ce har yanzun ba a ciro ragowar mutane 15 ba.
Asali: Legit.ng