Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Bukaci Dakarun Sojoji Su Kakkabe 'Yan Ta'adda

Gwamnonin Arewa Maso Gabas Sun Bukaci Dakarun Sojoji Su Kakkabe 'Yan Ta'adda

  • Ƙungiyar gwamnonin jihohin yankin Arewa Maso Gabas sun gudanar da taro domin nemo hanyoyin magance rashin tsaron da ya addabi yankin
  • Gwamnonin sun buƙaci dakarun sojoji da su bi ƴan ta'addan da suka ƙi miƙa wuya har maɓoyarsu su halaka su
  • Gwamnonin sun kuma yaba da ƙoƙarin da dakarun sojojin su ke yi wajen ganin cewa zaman lafiya ya dawo a yankin

Maiduguri, jihar Borno - Ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya, sun buƙaci dakarun sojoji da su farmaki maɓoyar ƴan ta'addan da suka ƙi miƙa wuya su halaka su.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gwamnan jihar Borno kuma shugaban ƙungiyar, Farfesa Babagana Umara Zulum, shi ne ya yi wannan kiran a wajen taron ƙungiyar karo na takwas, ranar Asabar, 9 ga watan Satumba a birnin Maiduguri.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Bayyana Muhimmin Dalili 1 Da Yakamata Atiku/Peter Obi Su Amince Da Hukuncin Kotu

Gwamna Zulum ya yaba wa jami'an tsaro
Gwamnonin Arewa Maso Gabas sun bukaci dakarun sojoji su kakkabe yan ta'adda Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

Zulum, wanda ya yaba wa jami'an tsaro bisa zaman lafiyan da ya fara dawowa a yankin, ya bayyana cewa akwai buƙatar a kakkaɓe ragowar ƴan ta'addan da suka ƙi ajiye makamansu, rahoton Tribune ya tabbatar.

Gwamna Zulum ya yaba wa jami'an tsaro

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Bari na yi amfani da wannan damar wajen yaba wa jajirtattun jami'an tsaron mu wajen yaƙi da ta'addancin da su ke yi da ƙoƙarin da su ke na samun nasara.
"Ko tantama babu sun yi amfani da hanyoyi da dama wajen yaƙi da ta'addancin, inda suka samu cigaba sosai wanda yake nuna cewa ƙarshen ta'addanci a yankin na dab da zuwa."
"Ina son yin kira ga dakarun sojojin Najeriya su kutsa maɓoyar ƴan ta'adda waɗanda ba su shirya miƙa wuya ba. Dole ne mu koro su daga maɓoyarsu domin halaka waɗanda suka ƙi yarda su ajiye makamansu."

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Bayyana Yankunan Da Za Su Ci Gajiyar Mulkin Shugaba Tinubu

Gwamnan wanda ya koka kan koma bayan da ta'addanci ya kawo a yankin ta hanyar dakatar da harkokin kasuwanci da sauran abubuwa, ya bayyana cewa idan har ba an daƙile ƴan ta'addan ba, duk wani ƙoƙarin gyara abubuwa ba zai yi tasiri ba.

Tinubu Zai Sake Gina Arewacin Najeriya

A wani labarin na daban, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ware maƙudan kuɗi har biliyan 50, domin sake gina Arewacin Najeriya.

Shugaba Tinubu ya ware kudaden ne musamman domin yankunan Arewa maso Yamma da kuma Gabas wadanda su kafi fuskantar matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng