Wani Bature Ya Canja Dala Daya Zuwa Naira, Ya Kwashi Kayan Dadi Da Abunsa
- Wani bature wanda ke watsa shirye-shirye kan rayuwa a Najeriya da al'adun kasar ya siya abubuwa da dama da dala daya
- Mutumin ya cika tumbinsa da kayan filawa dangin su cincin kafin ya siyi taliya, wake da kwai
- Yan Najeriya da dama da suka kalli bidiyonsa sun nuna shakku kan cewa ya siya abubuwa a farashi mai sauki, wasu sun ce an dai yi masa ragi ne
Wani bature mai suna Chris wanda ke yin bidiyoyi masu kayatarwa kan Najeriya da mutanenta ya sake yin wani.
A sabon bidiyon, mutumin ya canja kudi dala daya sannan kudin ya kama N900 da aka mayar da shi naira. Ya yi amfani da kudin wajen more rayuwa a gari.
Abubuwan da kudin suka siya masa
Mutumin ya siya cincin din N100. Daga nan ya sake siya puff puff shima na wannan farashin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bayan kayan filawa, Chris ya siya shinkafa, taliya, wake da kwai na N400. Don ya gama da kudin nasa gaba daya, sai ya siya masara da sauran abubuwa.
Kalli bidiyon a kasa:
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama'a a kasa:
blessing ta ce:
"Don Allah wai a wannan Najeriyar da nake ne ko wata daban."
theBestest ta ce:
"Kana samun ragin farar fata. Kwai kadai 3100 yake ga taliya, ga wake!!!!"
Bolu ya yi mamaki:
"Wannan cincin din naira 100 yake?"
Ceedy Ekun ya ce:
"Farashin ba daidai bane don Allah yi hakuri!"
Betterpen ya ce:
"Kwai 150 ne ka cika karya Chris."
Natalia | Career + Life ta ce:
"Zan tafi Najeriya ta fi saukin rayuwa."
emaboss ya ce:
"Wai da gaske mutum zai iya ci ya koshi da @900."
“Kada Ku Kuskura Ku Bar Matayenku Ku Tafi Turai”: Dan Najeriya Da Ke Zaune a UK Ya Gargadi Ma’aurata
Farashin iskar gas ya tashi da kaso 9 yayin da ake tsadar fetur
A wani labari na daban, mun ji cewa yyin da ake ta murna cewa farashin iskar gas na saukowa, ashe abin lokaci ya ke jira.
Farashin gas ya tashi da kusan kaso 9 zuwa Naira 745 kan ko wane kilogiram daya yayin da ‘yan Najeriya ke kara shiga halin wahala, Legit.ng ta tattaro.
Shugaban kungiyar masu siyar da iskar gas (NALPGM), Olatunbosun Oladapo ya bayyana cewa ‘yan kasar za su fara biyan karin kudin gas daga tsakiyar watan Agusta.
Asali: Legit.ng