Kashim Shettima Ya Kara Ba 'Yan Najeriya Hakuri Kan Halin Matsin Da Ake Ciki

Kashim Shettima Ya Kara Ba 'Yan Najeriya Hakuri Kan Halin Matsin Da Ake Ciki

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana yankunan da za su ci gajiyar ayyukan gwamnatin Shugaba Tinubu
  • Shettima ya bayyana cewa dukkanin yankuna shida na ƙasar nan za su amfana daga ayyukan da gwamnatin Shugaba za ta yi
  • Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara yin haƙuri kan halin da ake ciki inda ya ce gwamnati na iya bakin ƙoƙarinta

Jihar Borno - Mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya bayyana cewa dukkanin yankunan Najeriya za su amfana da ayyukan cigaba na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa, Shettima ya bayar da wannan tabbacin ne a birnin Maidiguri a ranar Juma'a, 8 ga watan Satumba a fadar Shehun Borno, Alhaji Abubakar Umar-Garbai.

Kashim Shettima ya bayyana yankunan da su ci moriyar aikin Tinubu
Kashim Shettima ya ce kowanne yanki zai amfana da ayyukan Tinubu Hoto: Kashim Shettima
Asali: Facebook

Shettima ya bayyana cewa gwamnati tana sane da halin ƙuncin da ƴan Najeriya ke ciki, sannan tana ɗaukar matakai domin magance su gaba ɗaya, rahoton The Nation ya tabbatar.

Kara karanta wannan

"Kowace Jiha 1,000" Shugaba Tinubu Ya Amince da Muhimmin Aiki a Jihohi 7 Na Arewacin Najeriya

Ya bayyana wasu daga cikin matakai masu tsauri da gwamnatin ta ɗauka, sun faru ne a dalilin halin da ƙasar ta tsinci kanta a ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ina bayar da tabbacin cewa a cikin ƴan makonni da watanni masu zuwa, gwamnati za ta fito da shirye-shirye masu yawa da za su amfani rayuwar al'ummar mu." A cewarsa.
"Mun zo nan ne tare da ministan noma domin ganin shirin samar da alkama a Borno."

Tinubu zai gina gidaje a Arewacin Najeriya

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma sanar da amincewar Shugaba Tinubu domin gina gidaje 1000 a jihohin Sokoto, Kebbi, Zamfara, Kaduna, Neja da Benue.

Ya bayyana cewa gidajen za su samu ababen more rayuwa irin su, asibitoci, makarantu da wuraren kiwon dabbobi ga Fulani.

Ya buƙaci ƴan Najeriya da su ƙara haƙuri sannan su goya wa gwamnatin baya domin a shirye take ta share musu hawayensu.

Kara karanta wannan

"Ɗalibi Mai Hazaƙa" Daga Ƙarshe, Shugaba Tinubu Ya Bayyana Gaskiyar Tarihin Karatunsa a Jami'a

Atiju Ya Yi Wa Kashim Martani

A wani labarin na daban kuma, tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi wa Kashim Shettima, martani kan batun yi masa ritaya a siyasa.

Atiku wanda ya. takarar shugaban ƙasa a ƙarkashin inuwar jam'iyyr PDP zaɓen 2022, ya bayyana cewa lokacon yin rityarsa a siyasa bai yi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng