Ana Yajin Aiki, Gwamna Bago Ya Amince da Bai Wa Kungiyar NLC Motocin Shinkafa

Ana Yajin Aiki, Gwamna Bago Ya Amince da Bai Wa Kungiyar NLC Motocin Shinkafa

  • Gwamnan jihar Neja ya amince a bai wa ƙungiyar kwadago NLC Tirela biyu na shinkafa domin rage raɗaɗin cire tallafin fetur
  • Bago ya bayyana haka ne a wurin liyafar murna kan sabon ofishin mataimakin gwamna duk da NLC na cikin yajin aikin gargaɗi
  • Ya ce Naira miliyan 110 da gwamnatinsa ta tura wa NLC tun farko kuɗin aikin sanya ido ne kan yadda ake raba tallafi ga talakawa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Niger - Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya amince da tura tireloli biyu na buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 50 ga kungiyar kwadago ta kasa NLC reshen jihar.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa gwamna Bago na jam'iyyar APC ya bai wa NLC manyan motocin Shinkafar ne domin rage musu raɗaɗin cire tallafin man Fetur.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP Ya Samu Abinda Yake So, Zai Runtumo Wa Jiharsa Bashin Naira Biliyan 50

Gwamnan jihar Neja, Umar Bago.
Ana Yajin Aiki, Gwamna Bago Ya Amince da Bai Wa Kungiyar NLC Motocin Shinkafa Hoto: Tsalle Ɗaya
Asali: Facebook

Gwamna Bago ya bayyana haka ne a wurin liyafar da aka shirya a bikin murnar sabon ofishin mataimakin gwamna, Yakubu Garba, wanda ya gudana a Minna.

Ya ƙara da cewa Naira miliyan N110 da gwamnatinsa ta amince a bai wa NLC a farko, an ba su ne a matsayin kuɗin aikin sa ido kan rabon kayan tallafi a faɗin gundumomi 274 na jihar Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Umar Bago ya ce:

“Mambobin ƙungiyar kwadago, mun ba ku aikin zagayawa don kula da yadda ake rabon kayan tallafi, amma ba mu ba ku naku tallafin ba. Mun dai baku kuɗin da zaku zagaya lungu da saƙo."
"A halin yanzu, gwamnati zata baku manyan Tireloli maƙare da buhunan Shinkafa mai nauyin kilogram 50 domin ku raba a tsakaninku."

Bago ya kara da cewa kudin farko na mambobin NLC ne domin su sa ido sosai kan yadda ake rabon kayayyakin domin tabbatar da kayan abincin sun isa ga kowa da kowa.

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Kama Jami'an Gwamnati Da Ke Karkatar da Tallafin da Ake Raba Wa Talakawa

NLC na cikin yajin aikin gargaɗi

A halin yanzu dai kungiyar NLC na cikin yajin aikin gargadi na kwanaki biyu wanda ta ayyana sakamakon cire tallafin man fetur da kuma wahalhalun da suka biyo baya.

Gwamnan ya shawarci kungiyar kwadago da ta janye yajin aikin da take yi tare da taya mataimakin gwamnan murnar sabon ofishin da aka gina masa.

Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Tashi a Filin Jirgin Kasa da Kasa a Legas

A wani labarin kuma Wata Gobara ta turnuƙe wani ɓangaren filin jirgin sama na Murtala Muhammed da hayaƙi da safiyar ranar Laraba.

Rahoto ya nuna cewa hayaƙin wanda ya tashi da misalin ƙarfe 7:50 na safe, ya sanya mutane da ma'aikata guduwa daga wurin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262