Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Tashi a Filin Jirgin Kasa da Kasa a Legas

Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Tashi a Filin Jirgin Kasa da Kasa a Legas

  • Wata Gobara ta turnuƙe wani ɓangaren filin jirgin sama na Murtala Muhammed da hayaƙi da safiyar ranar Laraba
  • Rahoto ya nuna cewa hayaƙin wanda ya tashi da misalin ƙarfe 7:50 na safe, ya sanya mutane da ma'aikata guduwa daga wurin
  • Daraktan yaɗa labarai na FAAN ya tabbatar da cewa ƙoƙarin jami'an kwana-kwana ya sa komai ya dawo daidai a wurin

Lagos - An shiga yanayin tashin hankali a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed da ke jihar Legas yayin da wata Gobara ta kama ranar Laraba.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ibtila'in wutar, wanda ya auku ranar Laraba da misalin ƙarfe 7:50 na safe, ya sa Fasinjoji da ma'aikatan filin jirgin guduwar neman tsira.

Hayakin da ya tashi a filin jirgi a Legas.
Tashin Hankali Yayin da Gobara Ta Tashi a Filin Jirgin Kasa da Kasa a Legas Hoto: vanguard
Asali: UGC

Channels tv ta tattaro cewa hayaƙi ya tashi a ɓangaren Terminal 1 da ke filin jirgin Murtala Muhammed a Ikeja, babban birnin jihar Legas.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Ya Gana da Fitaccen Attajirin Duniya a Indiya, Bayanai Sun Fito

Haka nan kuma ana tsammanin hayaƙin ya taso ne daga ƙasan ginin Terminal ɗin amma tuni muhukunta suka kai ɗauki kuma suka shawo kan lamarin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wane mataki aka ɗauka kan lamarin?

Daraktan yaɗa labarai na FAAN, Abdullahi Yakubu-Funtua, ya ce kokarin da jami'an kwana-kwana na filin jirgin suka yi, ya taimaka wajen shawo kan lamarin nan take.

Yakubu Funtua ya ce:

"Nan take jami'an hukumar kwana-kwana da ke aiki a filin jirgin Murtala Muhammed (ARFFS) suka kai ɗaukin gaggawa wurin, kuma kokarinsu ya taimaka wajen shawo kan lamarin."
“Kamar yadda muka saba jajirce wa wajen tabbatar da lafiyar fasinjoji, ma’aikata, da duk masu amfani da filin jirgin, nan take aka kawar da Terminal ɗin bayan hayakin da ya mamaye wasu wuraren ginin."
"Muna farin cikin tabbatar da cewa a halin yanzun komai ya daidai ta, kuma FAAN ba zata yi ƙasa a guiwa ba a koƙarin tabbatar da aminci, kwanciyar hankali da tsaro."

Kara karanta wannan

Hukumar DSS Ta Kama Jami'an Gwamnati Da Ke Karkatar da Tallafin da Ake Raba Wa Talakawa

Ƙungiyar Kwadago NLC Ta Kawo Babban Cikas a Shirin Yanke Hukuncin Kotun Zabe

Kun da labarin an samu jinkiri a zaman Kotun sauraron kararrakin zaben 'yan majalisar tarayya mai zama a Kotun sakamakon yajin aikin NLC.

Ma'aikatan shari'a sun garƙame Kofar shiga Ƙotun wacce ta shirya yanke hukunci kan zaben Sanatan Ogun ta yamma ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262