Gwamnatin Jihar Abia Ta Musanta Batun Korar Ma'aikata 10,000 Daga Aiki
- Gwamnatin jihar Abia ta musanta batun cewa ta datsewa ma'aikata 10,000 hanyar neman samun na cin abincinsu
- Gwamnatin ta bayyana cewa ma'aikatan da aka sallama na bogi ne da waɗanda ba a bi ƙa'ida ba wajen ɗaukarsu aiki
- Kwamishinan watsa labaran jihar Okey Kanu wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana cewa ma'aikatan an saɓa ƙa'idoji wajen ɗaukarsu aiki
Jiihar Abia - Gwamnatin jihar Abia ta musanta rahotannin cewa ta kori ma'aikata 10,000 daga aiki.
Kwamishinan al'adu da watsa labarai na jihar, Okey Kanu, shi ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da manema labarai a ranar Laraba, 6 ga watan Satumban 2023, rahoton PM News ya tabbatar.
"Rahoton cewa gwamna Alex Otti ya kori ma'aikata babu ƙamshin gaskiya a cikinsa." A cewarsa.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta fito da wasu matakai domin magance matsalar ma'aikatan bogi, inda ya ƙara da cewa a dalilin hakan ne gwamnatin ta cire sunayen ma'aikatan bogi daga cikin albashinta, cewar rahoton Daily Post.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Menene dalilin korar wasu ma'aikatan?
"Wasu daga cikin ma'aikatan da sunayensu suka bayyana a wajen tantancewa ba a ɗauke su ta hanyar da ta dace ba, na daga cikin waɗanda abun ya shafa." A cewarsa.
"Wannan rukunin sun haɗa da waɗanda aka ɗauka aiki ba bisa ƙa'ida ba, a tsakanin watan Disamban 2022 har zuwa watannin Maris da Afirilu na wannan shekarar."
Kwamishinan ya bayyana cewa akwai hanyoyin da aka tsara wajen ɗaukar ma'aikata a jihar Abia.
Kanu ya bayyana cewa ba a bi ƙa'ida ba wajen ɗaukar su aiki sannan ya buƙaci al'ummar jihar Abia da su yi watsi da batun korar ma'aikata 10,000.
Gwamnan Jihar Gombe Ya Yi Karin Albashi
A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Gombe ya ƙarawa ma'aikatan jihar albashi, domin rage musu raɗaɗin da cire tallafin man fetue ya jawo a ƙasar nan.
Gwamna Inuwa Yahaya ya yi wa ma'aikatan ƙarin albashin N10,000 a kan kowane mataki a jihar, inda sabon tsarin albashin za a fara biyansa a watan Agusta.
Asali: Legit.ng