Jami'an NLC Da Ma'aikata Sun Ba Hammata Iska Kan Yajin Aiki a Jihar Ondo

Jami'an NLC Da Ma'aikata Sun Ba Hammata Iska Kan Yajin Aiki a Jihar Ondo

  • A ƙoƙarin tabbatar da bin umarnin yajin aikin gargaɗi na kwana biyu, jami'an ƙungiyar ƙwadago da ma'aikata sun ba hammata iska a jihar Ondo
  • Jami'an na NLC sun kuma kori wasu ma'aikata daga ofisoshinsu a jihar wacce take a yankin Kudu maso Yamma na Najeriya
  • Wasu ƴan Najeriya sun yi martani kan lamarin wanda aka yaɗa bidiyonsa a Twitter ranar Talata, 5 ga watan Satumba

Akure - Ƙungiyar ƙwadago (NLC) da wasu ma'aikata a jihar Ondo sun ba hammata iska kan yajin aikin gargaɗi na kwana biyu da ƙungiyar ta fara.

Ƙungiyar ƙwadago ta sanar da shiga yajin aikin gargaɗi na kwana biyu, biyo bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.

Jami'an NLC da ma'aikata sun yi fada a Ondo
Jami'an NLC da ma'aikata sun dambace kan yajin aikin gargadi a jihar Ondo Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

NLC, ma'aikata sun yi faɗa a Ondo

A ƙoƙarin tabbatar da bin wannan umarnin yajin aikin, an nuna jami'an NLC a cikin wani bidiyo da @TheNationNews ta sanya, suna korar ma'aikata daga ofisoshinsu, sannan a wani wajen har da yin bulala da ba hammata iska da ma'aikatan da suka fito wajen aiki.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Kungiyar Kwadago Reshen Jihar Kano Ta Sanar Da Sabbin Matakan Da Ɗauka

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ƴan Najeriya sun yi martani kan korar ma'aikata da NLC ta yi a Ondo

Wasu daga cikin ƴan Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu kan faɗan da korar ma'aikata da jami'an NLC suka yi a jihar Ondo.

@kingshoes_oh ya rubuta:

"Wai har taƙaddamar ta kai matsayin da NLC sai ta yi amfani da ƙarfi, menene abin da hakan zai haifar?"

@RashwalRashwal ya rubuta:

"Wannan bai dace ba ta kowacce fuska. A bar kowa ya yanke hukuncin da yake so."

@Engr_Stanley_EC ya rubuta:

"Ƙungiya mara amfani bayan APC ita ce NLC. Ka san haka ka zauna lafiya."

@jagabanolu ƴa rubuta:

"Wannan wane irin hauka ne?" NLC ta tilasta mutanen da ke son yin aiki sai sun shiga yajin aiki ba da son ransu ba. Tinubu da ƴan sanda yakamata su binciki lamarin nan da tuhumar NLC."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Tinubu Zata Gana da Ƙungiyoyin Kwadago Na Ƙasa Kan Muhimmin Abu 1

@thinktwiz ya rubuta:

"Waɗanda ke ta ganin laifinsu yakamata su san jarjejeriya da ke tsakanin ma'aikata da NLC. Bai yiwuwa ka yi zagon ƙasa sannan ka samu tarba irinta jarumai.

Kungiyar TUC Ta Fice Daga Yajin Aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar ƴan kasuwa ta (TUC) ta bayyana cewa ba ruwanta da shiga yajin aikin gargaɗi na kwana biyu wanda ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) za ta yi.

Ƙungiyar ta shawarci NLC da ta ƙarfafa tattaunawar da ta fara da gwamnati a maimakon shiga yajin aikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng