Gwamnan Delta Ya Nada Abokin Adawarsa Na NNPP a Matsayin Hadimi
- Gwamnan jihar Delta na jam'iyyar PDP ya naɗa sabbin masu ba shi shawara ta musamman guda 9
- Sakataren gwamnatin jihar, Kingsley Emu, ya bayyana cewa gwamnan ya naɗa abokin gwabzawarsa a zaben da ya gabata a muƙami mai girma
- Ya ce nan bada jimawa ba gwamnatin Sheriff Oborevwori zata sanar da ranar rantsar da sabbin hadiman
Delta - Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta ya naɗa ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar NNPP a zaben watan Maris da ya gabata, Goodnews Agbi, a matsayin mashawarci na musamman.
Sakataren gwamnatin jihar Delta (SSG), Kingsley Emu, shi ne ya tabbatar da haka ga manema labarai a Asaba, babban birnin jihar Delta, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Mista Emu ya kuma bayyana cewa baya ga ɗan takarar gwamnan, mai girma gwamna ya amince da naɗa sabbin masu ba shi shawara ta musamman guda 8, kamar yadda Vanguard a ta tattaro.
"In Ka Isa Ka Ƙaryata" Shugaban NNPP Ya Tona Cin Amanar Da Kwnakwaso Ya Yi Kwana 4 Gabanin Zaɓen 2023
Jerin mutanen da gwamnan Delta ya naɗa
SSG ya bayyana sunayen waɗanda Oborevwori ya naɗa a matsayin mashawarta na musamnan, ciki harda Michael Ogboru, ɗan Great Ovedje Ogboru, tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar APGA.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Haka zalika gwamnan ya naɗa, Ebikeme Clark, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Burutu kuma ɗan jagoran ƙungiyar PANDEV, Chief Edwin K. Clark, a matsayin mai bada shawara.
Oborevwori ya kuma amince da naɗin Mista Sylvester Oromoni, wanda aka kashe ɗansa ɗalibin makarantar kwalejin Dowen a Lekki, jihar Legas.
Sauran waɗanda gwamnan ya naɗa sun haɗa da, Charles Whomrowho Oniyere, Mista. Sylvester Oromoni, Honorabul Shedrack Ekene Rapu, Dakta Donald Onyibe Peterson, Honirabul Peter Uviejitobor da kuma Cif Nath Azuka Igbadi.
Yaushe za su fara aiki a sabon muƙamin?
Sakataren gwamnatin ya ƙarkare da cewa nan ba da jima wa ba za a sanar da ranar da mai girma gwamna zai rantsar da su domin fara aiki a sabbin ofisoshin su.
"Kwankwaso Matsala Ne a Siyasa" Sabon Shugaban NNPP Na Shiyyar Kudu
A wani rahoton kun ji cewa Rikicin jam'iyyar NNPP ya ƙara tsananta yayin da shugaban kudu ya tona cin amanar da Kwankwaso ya yi ana dab da zaɓen 2023.
Sabon shugaban NNPP na shiyyar Kudu maso Yamma, Alhaji Wasiu Ajirotutu, ya ce Kwankwaso ba abinda yarda bane a siyasa.
Asali: Legit.ng