Shugaba Bola Tinubu Ya Gana Da Manyan Hafsoshin Tsaro A Aso Vila
- Gabanin tafiya ƙasar Indiya, Shugaba Tinubu ya yi ganawa mai matukar muhimnanci da hafsoshin tsaro a Villa da ke Abuja
- Hafsoshin tsaron zasu yi wa Tinubu bayani kan halin da ake ciki yayin da ya cika kwanaki 100 da hawa kan madafun iko
- A ranar Litinin ɗin nan, Tinubu zai bar Najeriya zuwa ƙasar Indiya domin halartar taron G-20 a New Delhi
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan ranar Litinin, 4 ga watan Satumba, 2023 a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Ministocin tsaro da Hafsoshin tsaro sun yi wa shugaba Tinubu bayani kan halin da tsaron kasa ke ciki yayin da yake shirye-shiryen zuwa ƙasar Indiya.
Bola Ahmed Tinubu zai tafi ƙasar Indiya ne domin halartar taron G-20, inda zai haɗu da wasu shugabannin ƙasashen duniya.
Wannan shi ne karo na biyu da majalisar tsaron Najeriya ta gudanar da taro a fadar shugaban ƙasa tun bayan da Tinubu ya karɓi mulki ranar 29 ga watan Mayu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shugabannin hukumomin tsaron da suka halarci taron sun haɗa da, babban hafsan tsaron ƙasa (CDS), Janar Christopher Musa, da babban hafsan rundunar sojin ƙasa (COAS), Janar Taoreed Lagbaja.
Sauran mahalarta taron sun ƙunshi babban hafsan rundunar sojin saman Najeriya, Air Vice Marshal Hassan Abubakar da babban hafsan sojojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla, NTA News ta rahoto.
Wane batutun aka tattauna a wannan taron?
Rahotanni sun nuna cewa wannan taro na majalisar tsaron ƙasa ya maida hankali ne kan yanayin tsaron da ake ciki a faɗin sassan Najeriya.
Haka zalika ana hasashen mahalarta taron sun tattauna batutuwan da suka shafi bangarorin da ya kamata Hafsoshin tsaro su nunka kokarinsu domin tabbatar da zaman lafiya.
Tsohon Sanata Ya Yi Wa Atiku Wankin Babban Bargo Kan Kalubalantar Nasarar Tinubu, Ya Ba Shi Wata Muhimmiyar Shawara
Wannan gana wa na zuwa ne yayin da shugaba Bola Tinubu ke shirin tafiya ƙasar Indiya domin halartar taron G-20 wanda zai gudana a New Delhi a ranakun 9 da 10 ga watan Satumba.
Kwankwaso ya gana da Tinubu ana dab da zabe - Shugaban NNPP
A wani rahoton na daban kuma Sabon shugaban NNPP na shiyyar Kudu maso Yamma, Alhaji Wasiu Ajirotutu, ya ce Kwankwaso ba abinda yarda bane a siyasa.
Ya kuma kalubalanci Kwankwaso ya fito bainar jama'a ya musanta zargin cewa ya gana da ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, kwana huɗu gabanin zaɓe.
Asali: Legit.ng