Shugaba Tinubu Ya Sauke Jakadan Najeriya A Ƙasar Burtaniya
- Bola Ahned Tinubu ya sauke jakadan Najeriya a ƙasar Burtaniya daga muƙaminsa, ya buƙaci ya tafi hutun kwanaki 60
- A wata sanarwa da ministan harkokin ƙasashen waje ya fitar, ya ce shugaba Tinubu ya gode wa jakadan bisa aikin da ya yi wa ƙasa
- Matakin na zuwa ne kwana ɗaya bayan shugaban ƙasa ya naɗa matashi ɗan shekara 32 a matsayin shugaban hukumar NASENI ta ƙasa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sauke jakadan Najeriya a ƙasar Burtaniya (UK), Sarafa Isola, kana ya umarci ya dawo gida Najeriya, The Cable ta tattaro.
Sanarwar kiran dawo da jakadan na kunshe ne a cikin wata wasika mai ɗauke da sa hannun, Yusuf Tuggar, ministan harkokin waje, da kwanan watan 31 ga watan Agusta, 2023.
Ministan ya ce:
“Ina farin cikin sanar da kai matakin da shugaban kasa ya dauka na kiran ka dawo gida, wanda ke nuna karshen wa’adinka na jakadan Tarayyar Najeriya a kasar Birtaniya."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Bayan wannan saƙo, yanzu ana sa ran za ka fara shirin miƙa mulki, kana ka ɗauki hutu a hukumance na kwanaki 60, sannan ka dawo Najeriya nan da ranar 31 ga Oktoba, 2023."
Shugaba Tinubu ya gide wa jakadan
A madadin Tinubu, Tuggar ya gode wa jakadan bisa hidimar da ya yi wa ƙasa tare da yi masa fatan alheri a cikin ayyukan da zai tasa nan gaba, Premium Times ta rahoto.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne ya naɗa Mista Isola a matsayin babban jakadan Najeriya a kasar Birtaniya a watan Janairu, na shekarar 2021.
Haka kuma a baya Isola ya taba rike mukamin ministan ma’adinai da karafa a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa, Marigayi Alhaji Umaru Musa Yar’Adua.
Wannan mataki na zuwa ne awanni kaɗan bayan shugaba Tinubu ya tsige shugaban hukumar NASENI ta tarayya, inda ya maye gurbinsa da matashi ɗan shekara 32, Khalil Suleiman Halilu.
Man Fetur Zai Sauko Zuwa Ƙasa Da N200 a Kowace Lita Idan Aka Gyara Matatu, IPMAN
A wani labarin na daban kuma Shugaban ƙungiyar daillalan man fetur masu zaman kansu IPMAN ya ce 'yan Najeriya zasu iya sayen fetur kan N200 a kowace lita.
Joseph Obele, shugaban IPMAN na jihar Ribas ya ce hakan zata faru ne idan FG ta gyara matatun man cikin gida suka ci gaba da aiki.
Asali: Legit.ng