Man Fetur Zai Sauko Zuwa Ƙasa Da N200 a Kowace Lita Idan Aka Gyara Matatu, IPMAN
- Shugaban ƙungiyar daillalan man fetur masu zaman kansu IPMAN ya ce 'yan Najeriya zasu iya sayen fetur kan N200 a kowace lita
- Joseph Obele, shugaban IPMAN na jihar Ribas ya ce hakan zata faru ne idan FG ta gyara matatun man cikin gida suka ci gaba da aiki
- Ya ce amma idan haka bata samu ba, farashin fetur zai ci gaba da ƙaruwa sakamakon canjin yanayin kasuwa
FCT Abuja - Shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar man futur masu zaman kansu reshen jihar Ribas, Joseph Obele, ya roƙi gwamnatin tarayya ta tabbatar da an gyara matatun man cikin gida.
Ya bayyana cewa farashin man PMS wanda aka fi sani da Fetur zai sauko ya dawo ƙasa da Naira 200 kan kowace Lita idan matatun man Najeriya suka ci gaba da aiki.
Wannan na zuwa ne bayan gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dakatar da biyan tallafin man fetur, wanda ya haddasa tashin farashin litar mai da tsadar rayuwa.
Domin farfaɗo da tattalin arziƙin kasa, shugaba Tinubu ya yi alƙawarin tabbatar da matatar man Patakwal ta fara tace ɗanyen mai a watan Disamba, 2023.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A ranar Juma’a, karamin Ministan Albarkatun Man Fetur (Mai), Sanata Heineken Lokpobiri, a ziyarar da ya kai matatar man Fatakwal, ya jaddada kudirin FG na ganin matatar ta ci gaba da aiki.
Yadda farashin fetur zai dawo ƙasa da N200
Sai dai Obele, a wata hira da ya yi da jaridar Punch ranar Asabar, ya nuna damuwarsa kan yadda karancin dala ke ci gaba da shafar masu shigo da kaya.
Ya kara da cewa farashin fetur zai ci gaba da karuwa idan gwamnati ta kasa lalubo mafita cikin ƙanƙanin lokaci, jaridar Ripples ta tattaro.
A kalamansa, shugaban IPMAN ya ce:
"Matuƙar matatun mai na kasarmu ba su aiki, farashin lita zai ci gaba da karuwa saboda canjin yanayi. Amma idan matatun mu suka fara aiki, ‘yan Najeriya za su sayi mai kasa da Naira 200 kan kowace lita."
“Ƙarancin dala ya sa da wahala masu shigo da man fetur su ci gaba da shigo da shi daga waje. Kimanin makonni biyu ke nan ana cikin wannan yanayi."
Zan Bayyana Masu Hannu a Kashe-Kashen Rayuka Nan Da Makonni, Gwamna Uzodinma
A wani rahoton kuma Gwamna Uzodinma na jihar Imo ya lashi takobin bayyana masu ɗaukar nauyin kashe-kashen mutane a jihar.
Shugaban ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC ya nanata cewa matsalar tsaron jiharsa siyasa ce kuma masu kitsa lamarin sun san kansu.
Asali: Legit.ng