Kwara: Yan Sanda Sun Kama Malamin Musuluncin Da Suke Nema Ruwa a Jallo

Kwara: Yan Sanda Sun Kama Malamin Musuluncin Da Suke Nema Ruwa a Jallo

  • Jami'an rundunar 'yan sanda reshen jihar Kwara sun kama Malamin addinin Musuluncin nan da ake nema ruwa a jallo
  • Hukumar 'yan sanda ta nuna Malamin mai suna, Ayodeji Sala, a hedkwatar ta da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara
  • An ayyana neman Malamin ruwa a jallo ne biyo bayan barazanar da ya yi wa wasu mabiya Addinin gargajiya

Ilorin, Jihar Kwara - Wani Malamin Addinin Musulunci, Ayodeji Sala, wanda rundunar 'yan sanda reshen jihar Kwara ta ayyana nemansa ruwa jallo ya shiga hannun jami'ai.

Jaridar Punch ta tattaro cewa rundunar tana neman malamin ne bisa zargin yi wa wasu 'yan addinin gargajiya barazana a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.

Malamin Musuluncin nan da ake nema a Kwara ya shiga hannu.
Kwara: Yan Sanda Sun Kama Malamin Musuluncin da Suke Nema Ruwa a Jallo Hoto: punchng
Asali: UGC

A ranar Laraba da ta gabata, rundunar 'yan sandan ta bayyana Malamin a hedkwatar 'yan sanda da ke Ilorin, ta ce jami'an sun kama shi ne da yammacin Talata.

Kara karanta wannan

Allahu Akbar: Fitacciyar Malamar Addini Ta Gane Gaskiya, Ta Karɓi Addinin Musulunci a Arewacin Najeriya

Rundunar ta kuma kara da cewa jami'an 'yan sanda sun samu nasarar kama Malam Ayodeji a wani wuri da ya gudu ya ɓuya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Malamin ya bada hakuri

Da yake jawabi a lokacin da ‘yan sanda suka bayyana kama shi, Malam Sala ya ce bai san cewa abinda ya aikata na da hadari kuma yana iya haifar da rashin zaman lafiya ba.

Malamin, wanda fuskarsa ta nuna yana cikin nadama da neman yafiya, ya ce ko kaɗan ba kwamishinan 'yan sandan jihar, Ebunoluwarotimi Adelesi, bane ya tura shi ya yi wa 'yan addinin gargajiya barazana.

Ya ce duk ikirarin da ya yi a bidiyon da ke yawo cewa kwamishina ne ya turo shi ba gaskiya bane, domin bai ma san cewa zai je wurin mabiya addinin gargajiyan ba.

Ya roki ‘yan Najeriya, gwamnatin jihar, rundunar ‘yan sandan da kuma ‘yan gargajiya da lamarin ya shafa su yafe masa, inda ya ce bai taɓa shiga hannun jami'an tsaro ba.

Kara karanta wannan

Kishi: Wani Matashin Saurayi Ya Buga Wa Budurwarsa Guduma Har Lahira Kan Abu 1

Tun da fari dai Ayodeji ya yi barazana ga mabiya addinin gargajiya a lokacin da ya ziyarci shagon su da ke Ilorin, kamar yadda Sahara Reporters ta tattaro.

Jiragen Sojoji Guda Biyu Sun Yi Hatsari

A wani labarin kuma Jami'an soji 6 sun kwanta dama yayin da wasu jiragen sojoji masu saukar ungulu suka yi hatsari ranar Alhamis.

Bayanai sun nuna cewa jiragen sun faɗo ne yayin da suke atisayen yaƙi a gabashin ƙasar Ukraine.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262