Talauci Ne Babban Abinda Ke Haddasa Juyin Mulki a Nahiyar Afirka, Falana
- Babban lauyan nan ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin Bil'Adama, Femi Falana, ya bayyana babban abinda ke haddasa juyin mulki a Afirka
- Lauyan ya bayyana cewa yawan talauci ne ke jawo ƙaruwar juyin mulkin da sojoji ke yi a nahiyar Afirka
- Falana ya caccaki shugabannin Najeriya da nuna halin ko in kula da matsin rayuwar da al'umma suka tsinci kansu
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Fitaccen lauyan nan mai fafutukar kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN) ya ce yawan talaucin da ya addabi nahiyar Afirka ne ke haddasa ƙaruwar juyin mulki.
Channels tv ta tattaro cewa Lauyan ya yi wannan furuci ne a wurin wani taro da ƙungiyar Kwadago ta ƙasa (NLC) ta shirya wanda ya gudana a Abuja ranar Alhamis.
Falana ya kuma zargi masu rike da madafun iko a Najeriya da nuna halin ko in kula da kuma ɗaukar mutanen kasar ba a bakin komai ba.
A cewarsa, duk da talaucin da 'yan Najeriya da dama ke fama da shi a kasar, majalisar tarayya ta ware wa kanta biliyoyin kudi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Taken taron na bana shi ne "Tattalin Arzikin Najeriya da ƙalubalen rayuwa, Satar dukiyar talakawa domin ɗaga Masu Arziki".
Wannan kalamai na Falana na zuwa ne a daidai lokacin juyin mulkin sojoji ke ƙaruwa a tsakanin ƙasashen nahiyar Afirka.
Sojoji sun kifar da gwamnati a Gabon
Na ƙarshe da aka yi shi ne na ƙasar Gabon, wanda Sojoji suka kifar da gwamnatin shugaban ƙasa, Ali Bongo, suka kawo ƙarshen mulkin iyalan gidan Bongo na tsawon shekaru.
A ranar Asabar ɗin da ta gabata, aka gudanar da zabe a ƙasar Gabon kuma hamɓararren shugaban ƙasar ne ya samu nasara, sai dai sojojin sun soke zaɓen.
Wannan ci gaban ya janyo Allah wadai daga ƙasashe daban-daban a ciki da wajen nahiyar Afirka, kamar yadda Leadership ta tattaro.
Shugaba Tinubu Ya Maida Martani Kan Sabon Juyin Mulkin da Sojoji Suka Yi a Gabon, Ya Faɗi Mataki Na Gaba
A nasa ɓangaren, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi Allah wadai da juyin mulkin, inda ya ayyana yawan kwace mulki da ƙarfin bindiga da "yaɗuwar mulkin kama karya."
Har Yanzun Akwai Yan Najeriya Sama da 23,000 da Suka Ɓata, FG
A wani labarin na daban kuma Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa har yanzun akwai adadin mutane aƙalla 23,000 da suka ɓata a faɗin ƙasar nan.
Ministar jin ƙai da yaye talauci, Dakta Betta Edu ce ta bayyana haka a wurin taron ranar mutanen da suka ɓace wanda ya gudana a hukumar kare haƙƙin ɗan adam da ke Abuja.
Asali: Legit.ng