Juyin Mulkin Gabon: Atiku Ya Bayyana Yadda Za Kawo Karshen Kwace Mulki Da Sojoji Ke Yi a Afrika

Juyin Mulkin Gabon: Atiku Ya Bayyana Yadda Za Kawo Karshen Kwace Mulki Da Sojoji Ke Yi a Afrika

  • Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, ya yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar Gabon
  • Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce juyin mulkin Gabon shine irinsa na takwas da ya faru tun 2020, yana mai cewa ya kamata mutane su magance annobar a nahiyar
  • Atiku ya kuma bukaci ECOWAS da AU da su fara tattaunawa da shugabannin soji a kasashen da abun ya shafa don su koma bariki

Atiku Abubakar, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, ya yi Allah wadai da juyin mulkin da sojoji suka yi a Gabon, kasar da ke Afrika ta tsakiya.

A wata wallafa da ya yi a ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, tsohon mataimakin shugaban kasar ya nuna damuwa game da yawan juyin mulki da sojoji ke yi a Afrika, cewa ya kamata nahiyar ta mayar da hankali wajen magance cutar maimakon alamunta.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Faɗawa ECOWAS Da AU Abinda Ya Kamata Su Yi Dangane Da Juyin Mulki

Atiku ya yi watsi da juyin mulkin sojoji a Gabon
Juyin Mulkin Gabon: Atiku Ya Bayyana Yadda Za Kawo Karshen Kwace Mulki Da Sojoji Ke Yi a Afrika Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Twitter

A safiyar ranar Laraba, 30 ga watan Agusta ne, wasu jami'an sojoji a Gabon suka sanar da kwace mulki sannan suka soke zaben da aka yi kwanan nan a kasar.

Sojojin Gabon sun rufe boda

Sojojin sun kuma rufe iyakokin kasar sannan suka rufe duk hukumomin kasar yayin da aka gaggauta dakatar da tsarin doka.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai Atiku ya bayyana cewa matakin sojojin Gabon shine irinsa na takwas a nahiyar Afrika tun 2020, yana mai cewa dole a magance lamarin.

Jigon na PDP ya ce:

"Juyin mulkin baya-bayan nan ya kawo adadin juyin mulki da sojoji suka yi a Afrika ta tsakiya da yamma zuwa 8 tun 2020. Wannan abun damuwa ne kuma kira ne ga duba cikin gida. Watakila zai zama dole mu mayar da hankali wajen magance cutar ba wai alamomin da ke haifar da juyin mulki ba."

Kara karanta wannan

Fargabar Juyin Mulki: Rwanda, Kamaru Sun Dauki Tsauraran Matakai Kan Rundunar Tsaronsu, Sun Bayyana Matakan

Ya zama dole mu hana sojoji karbe mulki a Afrika

Atiku ya kara da cewar an fi son damokradiyya da mulkin damokradiyya kuma cewa ya kamata mutane su rungume shi tare da raya shi.

Ya kuma bukaci kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) da kungiyar AU su fara tattaunawa da shugabanni soji a kasashen da abun ya shafa domin su koma bariki.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce:

"Ya kamata hukumomin ECOWAS da na Tarayyar Afirka (AU) su bude kafar tattaunawa na diflomasiyya wanda zai ba sojojin damar komawa sansanin sojoji."

Ga wallafarsa a kasa:

Gabon: MURIC ta gargadi sojojin Najeriya kan juyin mulki

A wani labarin kuma, mun ji cewa kungiyar Kare Hakkin Musulmi (MURIC) ta shawarci rundunar sojojin Najeriya da kada ta yi koyi da sojojin Gabon da suka hambarar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo a ranar Laraba.

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya bayar da shawarar a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng