Yan Gudun Hijira Mutum 7 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya Bayan Gini Ya Rufto Musu a Borno

Yan Gudun Hijira Mutum 7 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya Bayan Gini Ya Rufto Musu a Borno

  • Tsautsayi ya faɗa kan wasu ƴan gudun hijira a jihar Borno bayan ginin ajin da su ke ciki ya rufto a kansu
  • Rayukan ƴan gudun hijira mutum shida ne suka salwanta yayin da.wasu da dama suka samu raunika
  • Ginin dai ya rufto ne a dalilin ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da aka ɗauki lokaci mai tsawo ana yi

Jihar Borno - Aƙalla mutum bakwai ne ƴan gudun hijira suka riga mu gidan gaskiya lokacin da ginin wani ajin da ke ɗauke da su a wata makaranta ya rufto a ƙaramar hukumar Monguno ta jihar Borno, cewar rahoton The Guardian.

Jaridar Leadership ta rahoto cewa majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa ajin wanda yake ɗauke da ƴan gudun hijirar masu yawa, ya rufto da misalin ƙarfe 7:00 na dare a ranar Litinin, a dalilin ruwan sama kamar da ƙwarya da ya auku ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Daga Karshe An Bayyana Abin Da Ya Haifar Da Tsadar Rayuwa a Najeriya

Gini ya rufto kan yan gudun hijira
Yan gudun hijira mutum 6 ne suka rasu a sanadiyyar ruftowar ginin Hoto: Leadership.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya auku

Majiyar ya ƙara da cewa huɗu daga cikin mutanen sun rasu ne a nan take, yayin da ragowar mutum biyun sun rasu ne a asibiti inda aka garzaya da mutum biyar waɗanda suka samu raunika.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Mutum huɗu daga cikinsu sun rasu ne nan take a wajen, mutum biyar sun samu raunika inda aka garzaya da su zuwa asibiti, daga baya mutum biyu daga cikinsu sun rasu." A cewarsa.

Lokacin da aka tuntuɓi shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Borno (BOSEMA), Kwamared Abdullahi Suleiman, ya bayyana cewa rahoton lamarin bai iso gaban hukumar ba, amma ya yi alƙawarin yin bincike sannan ya fitar da bayanai.

Dalilin ruftowar ginin

Lamarin dai ya auku ne a wata makarantar firamare da aka mayar da ita sansanin ƴan gudun hijira, inda ƴan gudun hijira masu yawa ke zaune a wajen sannan ajin da ya rufto ya rage ƙarfi a dalilin gobara da aka taɓa yi da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da ake yi a yankin.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sake Kai Farmaki a Zariya, Sun Yi Awon Gaba Da Bayin Allah

Monguno tana da babban sansanin ƴan gudun hijira da ya zama mafaka ga ƴan gudun hijiran da har yanzu akwai ƴan ta'addan Boko Haram a ƙananan hukumominsu.

Wike Ya Ziyarci Benen Da Ya Rufto a Abuja

A wani labarin na daban kuma, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya ziyarci wurin da bene mai hawa biyu ya rufta a Abuja.

Wike ya nuna takaicinsa kan aukuwar lamarin sannan ya bayar da umarnin a cafke mamallakin benen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng