Juyin Mulkin Nijar: Shugaba Tinubu Ya Tarbi Wakilan Amurka, Ya Bayyana Matsayar ECOWAS

Juyin Mulkin Nijar: Shugaba Tinubu Ya Tarbi Wakilan Amurka, Ya Bayyana Matsayar ECOWAS

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa yaƙi ba abun so ba ne amma kare dimokuraɗiyya yana da muhimmanci wajen magance rikicin Nijar
  • Tinubu ya bayyana cewa ECOWAS ta yi nisa wajen ƙoƙarin magance rikicin na Nijar cikin kwanciyar hankali
  • Ya bayyana cewa matsayar da ECOWAS ta cimmawa shi ne ba za ta bari wani ya ɓata lokaci ba saboda son zuciya a Jamhuriyar Nijar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana dalilin da ya sanya ya goyi bayan ƙungiyar ECOWAS na amfani da ƙarfin soja a Nijar idan sojojin juyin mulkin ba su mayar da hamɓararren shugaban ƙasa Mohamed Bazoum kan kujerarsa ba.

Tinubu ya bayyana cewa babu wata ƙasa da ke zuga shi, face kawai zai kare muradun Najeriya ne wajen ƙoƙarin da ECOWAS take yi na magance rikicin na Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

Daga Karshe An Bayyana Abin Da Ya Haifar Da Tsadar Rayuwa a Najeriya

Shugaba Tinubu ya yi magana kan rikicin Nijar
Shugaba Tinubu ya yi sabon bayani kan rikicin Nijar Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Ƙare dimokuraɗiyya a Nijar yana da muhimmaci

Shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin wakilin shugaban ƙasar Amurka da mataimakin sakataren Amurka kan harkokin Afirika, Molly Phee, a fadar shugaban ƙasa ranar Asabar, 26 ga watan Agusta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar a shafin Twitter na shugaban ƙasar Najeriya @NGRPresident.

Tinubu ya ƙara da cewa rikicin na Jamhuriyar Nijar ba zai sanya shi ya kasa kammala yin garambawul kan tattalin arziƙin ƙasar nan ba domin amfanin ƴan Najeriya.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Mun yi nisa a cikin ƙoƙarin da mu ke yi na warware rikicin Nijar cikin kwanciyar hankali ta hanyar amfani da hanyoyin diflomasiyya da mu ke da su. Na cigaba da dakatar da ECOWAs duk kuwa da cewa a shirye take kan ɗaukar kowane irin mataki, domin ganin an ƙarar da sauran hanyoyin warware rikicin."

Kara karanta wannan

"Ba Zai Yiwu Ba": Sojojin Nijar Sun Bayyana Dalilin Kin Dawo Da Bazoum Kan Mulki

"Yaƙi ba abun so ba ne dangane da shirye-shiryen tattalin arziƙin da na ke da su, amma kare dimokuraɗiyya ya zama dole. Matsayar ECOWAS ita ce ba za mu bari wani ya yi ɓata lokaci ba saboda son zuciya."

Sojojin Nijar Sun Umarci Dakaru Su Tsaya Cikin Shiri

A wani labarin kuma, gwamnatin sojojin Jamhuriyar Nijar ta umarci dakarunta da su kasance cikin shirin ko ta kwana.

Sojojin sun umarci dakarun ne domin gujewa fuskantar harin bazata, wanda ƙungiyar ECOWAS ke barazanar kai wa a ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng