Ana Tsaka da Nuna Adawa Ganduje Ya Rantsar da Meseko da Wasu 5 a Matsayin Jami’an NWC Na APC

Ana Tsaka da Nuna Adawa Ganduje Ya Rantsar da Meseko da Wasu 5 a Matsayin Jami’an NWC Na APC

  • Shugaban APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi sabbin nade-nade a jam’iyyar mai mulkin kasa a yanzu
  • An ruwaito cewa, an nada sabbin jami’an kwamitin ayyuka na APC a wasu jihohin Najeriya guda uku, kamar yadda rahoto ya kawo
  • Ana ci gaba da kai ruwa rana game da kasancewar Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC mai mulkin kasa

FCT, Abuja - Jam’iyyar APC ta rantsar da sabbin jami’ai shida a hukumance a kwamitin ayyukanta na kasa (NWC) duk da tsananin adawa da jam’iyyar da ke fuskanta a jihohin Kogi da Abia da kuma Cross River.

Taron na tsawon sa’a daya wanda shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje ya jagoranta, an yi shi ne a hedikwatar jam’iyyar ta kasa da misalin karfe 8:45 na yammacin ranar Juma’a, TV360 Nigeria ta tattaro.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Yi Magana Kan Sabon Rikicin Da Ya Ɓarke a Jam'iyyar APC, Ya Gana da Gwamnan Arewa

Wannan ci gaban na zuwa ne biyo bayan zanga-zangar da gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello, tsohon Sanata mai wakiltar Cross River ta Kudu da kuma Abia a APC suka yi.

Ganduje ya yi nadi a APC
An nada sabbin shugabannin NWC a APC | Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Dukkanin bangarorin uku, sun bayyana zaben jami’an a matsayin wani mataki da ya sabawa sunayen wadanda suka mikawa jam’iyyar mai mulki.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Su wa Ganduje ya rantsar?

Wadanda aka rantsar din sun hada da mataimakin shugaban APC na kasa a Arewa, Ali Bukar Dalori (jihar Borno) da Mataimakin Shugaban APC ma kasa na Arewa maso Yamma, Garba Datti Muhammad (Jihar Kaduna).

Hakazalika, akwai mai jam’iyyar APC shawari na kasa kan harkokin shari’a, Farfesa Abdul Karim Abubakar Kana (Jihar Nasarawa) da Sakataren walwala na APC na kasa, Donatus Nwankpa (Jahar Abia).

Sai kuma shugabar matan jam’iyyar ta kasa, Mary Alile Idele, PhD (Jihar Edo) da kuma, mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa, Duro Meseko (jihar Kogi), rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Rikicin Cikin Gida Ya Hargitsa NNPP, An Kori Wanda Ya Kafa Jam’iyya a 2002

Cece-kuce tun bayan zuwan Ganduje

Tun bayan nada Ganduje a matsayin shugaban APC ake ci gaba da cece-kuce da ganin bai cancanci wannan babbar kujera ta shugabancin APC ba.

Ganduje dai cikakken dan APC ne da ya mulki jihar Kano na tsawon zangon mulki biyu a karkashin jam’iyyar mai alamar tsintsiya.

Hakazalika, yana daya daga cikin tsoffin gwamnonin da suka fi daukar hankalin jama’a a Najeriya, duba da yawan zargin da ake masa na hannu ayyukan rashawa da cin hanci a lokacin gwamnatinsa.

Ganduje ya gyara zama a APC

A wani labarin, sabon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje ya nada wanda zai zama shugaban ma’aikata a ofishinsa.

Premium Times ta ce Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya tafi da Malam Muhammad Garba a matsayin shugaban ma’aikatansa a APC.

Kafin yanzu Muhammad Garba ya kasance Kwamishinan yada labarai a lokacin da Dr. Abdullahi Ganduje ya yi Gwamna a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Tsohon Hadimin Buhari Ya Yabawa Kokarin Gwamna Abba Gida Gida a Jihar Kano

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.