Tallafin Rage Radadi: Gwamnan Arewa Ya Bai Wa Yan Bautar Kasa Miliyan 36 Da Buhuhunan Shinkafa 100

Tallafin Rage Radadi: Gwamnan Arewa Ya Bai Wa Yan Bautar Kasa Miliyan 36 Da Buhuhunan Shinkafa 100

  • Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ba yan bautar kasa da NYSC ta tura Maiduguri tallafin rage radadi na naira miliyan 36.4
  • Kowani mutum daya daga cikin masu yi wa kasa hidima 1,215 zai tashi da N30,000
  • Zulum ya kuma ba masu yi wa kasar hidima buhuhunan shinkafa dari, buhuhunan wake 10 da shanaye don girka masu abinci

Jihar Borno - Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno, ya sanar da ware naira miliyan 36.4 ta yadda za a rabawa yan bautar kasa 1,215 da hukumar NYSC ta tura jihar N30,000 kowannensu a matsayin tallafin rage radadi.

Zulum, wanda ya ziyarci sansanin masu yi wa kasar hidima a Maiduguri, babban birnin jihar a ranar Asabar, 26 ga watan Agusta, ya ba yan bautar kasar tabbacin samun kariya, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Albashi Da Allawus Din Ministocin Tinubu Ya Bayyana, Za Su Lakume Biliyan 8.6

Zulum ya bai wa yan bautar kasa tallafin rage radadi
Tallafin Rage Radadi: Gwamnan Arewa Ya Bai Wa Yan Bautar Kasa Miliyan 36 Da Buhuhunan Shinkafa 100 Hoto: Daily Trust/ Twitter/@ProfZulum
Asali: UGC

Yan bautar kasa a Borno za su samu 30,000 kowannensu

Ya bayar da buhuhunan shinkafa 100, shanaye 10, manyan buhuhunan wake na 100kg guda 10, da galolin mai 10 domin dafawa yan hidimar kasar abinci na musammnan yayin zaman mako uku da za su yi a sansanin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya ce:

“Muna son mika tallafin rage radadi ga yan bautar kasa. Kowanne daga cikinku zai samu N30,000, za a tura wannan kudi asusun bankunanku da zaran an gabatar mun da bayanan bankinku.
"Kari a kan haka, mun samar maku da buhuhunan shinkafa 100, buhuhunan wake yan 100kg guda 10, galolin man gyada 10 da shanaye 10."

Ku zamo masu kiyaye dokoki da biyayya, Zulum ga yan bautar kasa

Ya bukaci masu yi wa kasar hidima da su kiyaye dokoki ta hanyar zama lafiya da junansu da kuma yin abubuwan da za su kawo zaman lafiya a kasar, rahoton New Telegraph.

Kara karanta wannan

Elon Musk Ya Samu Dala Biliyan 11 Cikin Dare Yayin Da Dangote Ya Yi Asarar Biliyan 43 A Kwana Daya

"Ina so ku zama jajirtattu kuma masu biyayya ga hukumomin da aka kafa. Ku yi abokai a yankunan kasar don tare ne za mu iya gina Najeriya mai ci gaba da bunkasa tattalin arziki mai dorewa."

Gwamnan ya nuna godiya ga gwamnatin tarayya kan inganta lamarin tsaro a Borno, wanda ya ba da damar dawo da sansanin NYSC a Maiduguri.

Tsawon shekaru 12, ba a bude sansanin NYSC a Maiduguri ba saboda ayyukan ta'addanci.

Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Sojojin Da Suka Ji Rauni Da Kyautar Kudi Miliyan 10

A wani labarin, gwamnan Borno, Babagana Zulum ya amince da sakin naira miliyan 10 a matsayin tallafi domin ragewa sojojin da suka ji rauni yayin yaki da ta'addanci a jihar radadi, jaridar Punch ta rahoto.

Wannan tallafi alkawari ne da Gwamna Zulum ya daukarwa sojojin watanni biyu da suka gabata a wajen taron cin abincin sallah wanda shugaban hafsan soji, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya shirya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng