Kasar Faransa Ta Daga Wa Sojin Nijar Yatsa, Ta Ce Babu Wanda Ya Isa Ya Kori Jakadanta a Jamhuriyar

Kasar Faransa Ta Daga Wa Sojin Nijar Yatsa, Ta Ce Babu Wanda Ya Isa Ya Kori Jakadanta a Jamhuriyar

  • Kasar Faransa ta yi watsi da umarnin sojin Nijar na fatattakar jakadanta a jamhuriyar dake cikin rikici
  • Sojin Nijar sun ba jakadan Faransa sa'o'i 48nya tattara kwamutsansa ya fice daga jamhuriyar da ke Yammacin Afrika
  • Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da kai ruwa rana kan yadda za a shawo kan rikicin da ke faruwa a Nijar

Paris, Faransa - Hukumomin kasar Faransa sun ce gwamnatin mulkin sojan Nijar ba ta da hurumin korar jakadanta a kasar Sylvain Itte, France 24 ta ruwaito.

Sojojin Nijar a ranar Juma'a sun ba ltte sa'o'i 48 ya fice daga jamhuriyar saboda kin amsa gayyatar da aka yi masa na ganawa da ministan harkokin waje da gwamnatin mulkin soji ta nada.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta ce matakin da gwamnatin Faransa ta dauka ya saba wa muradun Nijar.

Kara karanta wannan

Da gaske ne sojin Nijar sun kori jakadun Najeriya, Amurka da Jamus a kasarsu? Ga gaskiyar batu

Faransa ta yiwa Nijar martani mai zafi
Martanin Faransa ga Nijar | Hotuna: France 24
Asali: Facebook

Martanin Faransa mai zafi ga sojin Nijar

Sai dai Faransa ta ce sojojin na Nijar ba su da hurumin korar jakadanta a Yamai, kamar yadda Deutsche Welle ya nakalto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Faransa:

"'Yan harigido ba su da hurumin alanta wannan bukata, amincewar jakadan ka iya fitowa ne daga halastattun hukumomin Nijar.
"Muna ci gaba da tantance yanayin tsaro da aiki na ofishin jakadancinmu."

Bukatar Shugaba Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, a ranar Alhamis ya bukaci a sako shugaban Nijar Mohamed Bazoum wanda aka tsare a ranar 26 ga Yulin 2023.

An tsare Bazoum ne a wani juyin mulkin da sojoji suka yi karkashin jagorancin tsohon kwamandan dakarun tsaron Nijar, Abdourahamane Tchiani, rahoton The Guardian.

Macron, ya kuma yi kira da a koma kan tsarin dimokuradiyya a Nijar kamar yadda kasashen Nahiyar Afrika da dama a yanzu suke kai.

Kara karanta wannan

Rikici Ya Girma: Sojojin Nijar Sun Fusata, Sun Sake Ɗaukar Mataki Mai Tsauri Kan Ƙasar Faransa

Ba a kori jakadan Najeriya daga Nijar ba

A wani labarin, hukumar sojin Nijar ta umarci jakadan Faransa ne kadai ya fice daga kasar, ba jakadun Jamus, Amurka ko Najeriya ba, in ji sanarwar da ta fitar, rahoton Anadolu Agency.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin Juma'a, ma'aikatar ta yi watsi da rahotannin da ake yadawa da ke nuni da cewa an kori jakadun Jamus da Amurka da Najeriya, tare da bayyana cewa, Jakadan Faransa a Nijar ne kadai aka ayyana korarsa.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne gwamnatin mulkin sojan Nijar ta baiwa jakadan Faransa Sylvain Itte wa'adin sa'o'i 48 ya fice daga kasar, bisa zarginsa da kin amsa gayyatar da aka yi masa na ganawa da ministan harkokin wajen jamhuriyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.