Gwamnatin Sojin Nijar Ta Kori Jakadan Faransa, Ta Ba Shi Awanni 48
- Gwamnatin Nijar karƙashin jagorancin sojoji ta sanar da korar jakadan ƙasar Faransa, Sylvain Itte, daga cikin ƙasar
- A wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin ta bai wa jakadan Faransa wa'adin awanni 48 ya tattara kayansa ya fice daga Nijar
- Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da alaƙa ke ƙara tsami tsakanin sojojin Nijar da sauran ƙasashen ketare
Niger Republic - Gwamnatin sojin jamhuriyar Nijar ta kori jakadan ƙasar Faransa, Mista Sylvain Itte daga kasar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
Wannan matakin dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake takun saka tsakanin kasar da ke yammacin Afirka da kawayenta ƙasashen ƙetare.
Shugabannin sojojin Nijar da suka yi juyin mulki sun bai wa Jakadan Faransa wa'adin awanni 48 ya tattara komatsansa ya bar Jamhuriyar Nijar.
Meyasa Nijar ta kori jakadan Faransa?
A cikin wata sanarwa a ranar Juma'a, ma'aikatar harkokin wajen Nijar ta ce matakin korar jakadan ya samo asali ne daga kin mutunta gayyatar da aka yi masa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar, "Wasu ayyukan da gwamnatin Faransa ta yi wanda ya saba wa muradun Nijar" na daga cikin abinda ya jawo korar jakadan.
Sai dai duk da haka ma'aikatar wajen Jamhuriyar Nijar ba ta bada cikakken bayani kan wannan mataki ba, kamar yadda Reuters ta tattaro.
Gwamnatin Nijar na zargin Faransa da ECOWAS
Rundunar sojin Nijar ta zargi sojojin Faransa da sako ‘yan ta’adda da aka kama da kuma keta dokar hana zirga-zirgar jiragen sama a wani yunkuri na kawo cikas ga zaman lafiyar kasar.
Gwamnatin sojin ta kuma zargi kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) da hada dakarunta da wata kungiyar kasashen waje da ba ta ambaci sunanta ba.
Nijar, wacce Faransa ta yi wa mulkin mallaka, ta kasance abokiyar kawancen Faransa a yaƙin da take da mayakan jihadi kafin juyin mulkin watan da ya gabata.
Gwamnatin Nijar ta haɗa kai da sojojin ƙasashen Mali da Burkina Faso domin kare kanta daga barazanar ƙungiyar ECOWAS.
ECOWAS Ta Sake Tura Sako Ga Sojin Nijar
Kuna da labarin cewa Kungiyar Raya Kasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS ta kara bai wa sojin Nijar wata dama don sauya tunaninsu kan mika mulki.
Kungiyar na barazanar afkawa kasar da karfin soji idan ba su mika mulki cikin ruwan sanyi ba ga Shugaba Bazoum.
Asali: Legit.ng