Matatan Man Patakwal Zata Dawo Aiki a Watan Disamba, Ministan Tinubu
- Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta jaddata burinta na daina shigo da man fetur zuwa gida Najeriya nan da yan shekaru
- Ƙaramin ministan albarkatun fetur (Mai), Heineken Lokpobiri, ya ce a ƙarshen shekarar nan matatar Patakwal zata ci gaba da aiki
- Ya ce sauran matatun man Warri da Kaduna zasu biyo baya a shekara mai zuwa ga kuma matatar man Ɗangote
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Port Harcourt, Rivers - Gwamnatin Tarayya ta jaddada kudirinta na kawo karshen shigo da man fetur nan ba da daɗewa ba, inda ta ce ana kokarin dawo da aikin tace man fetur a cikin gida.
Ƙaramin ministan albarkatun man fetur (Mai), Sanata Heineken Lokpobiri, shi ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar duba aikin gyara matatar mai da ke Patakwal ranar Jumu'a.
Ministan ya kai wannan ziyara ne tare da takwaransa, karamin Ministan Man Fetur (Gas), Ekpeikpe Ekpo; da Babban Sakataren ma’aikatar albarkatun man fetur, Ambasada Gabriel T. Aduda.
Sauran waɗanda suka raka ministan sun haɗa da shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) da sauransu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yaushe matatun man Najeriya zasu ci gaba da aiki?
Ya ce idan aka yi la’akari da irin ci gaban da aka samu a aikin gyaran matatar Patakawal, ana sa ran zata dawo aiki a watan Disamba na wannan shekara.
A rahoton Tribune, Ministan ya ce:
"Manufarmu ita ce mu tabbatar da cewa nan da ’yan shekaru masu zuwa, Najeriya ta daina shigo da mai. Daga abin da muka gani a nan yau, matatar Patakwal za ta fara aiki a karshen shekara."
"Matatar Warri zata ci gaba aikin tace mai a karshen kwata na farko na shekara mai zuwa, sannan kuma matatar Kaduna za ta shigo cikin jirgin a karshen shekara mai zuwa."
"Idan aka haɗa da matatar Dangote, za mu iya dakatar da shigo da mai cikin ƙasar mu, kuma ‘yan Najeriya za su ci gajiyar dakatar da biyan tallafin mai.”
Umahi: Zan Zauna da Masu Kamfanoni Domin Rage Farashin Siminti
A wani labarin kuma Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin tattauna wa da masu kamfanonin siminti domin rage farashin kayayyakinsu.
Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce ‘ yan kwangila sun koka kan tsadar siminti a kasar nan, inda suka yi ikirarin cewa shigo da shi daga waje ya fi sauƙi da kuma arha.
Asali: Legit.ng