Shugaba Tinubu Ya Sake Tura Tawagar Malaman Addinin Musulunci Zuwa Nijar

Shugaba Tinubu Ya Sake Tura Tawagar Malaman Addinin Musulunci Zuwa Nijar

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika malaman addinin musulunci zuwa Jamhuriyar Nijar domin tattaunawa da shugaban gwamnatin soji, Janar Abdourahamane Tchiani
  • Shugaban ƙasar ya yanke wannan hukuncin ne a matsayinsa na shugaban ECOWAS bayan ya gana da malaman a Villa ranar Alhamis
  • Idan za a tuna dai, Abdulsalami Abubakarar, jagoran wakilan ECOWAS bayan ya dawo daga Nijar ya bayyana cewa tattaunawarsu da Tchiani ta haifar da ɗa mai ido

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da sake komawar malaman addinin musulunci zuwa Jamhuriyar Nijar domin sake tattaunawa da shugaban gwamnatin mulkin sojoji, Janar Abdourahmane Tchiani.

Shugaban ƙasar ya cimma wannan matsayar ne bayan ya gana da malaman addinin a ƙarkashin jagorancin Sheikh Dahiru Bauchi, a fadar shugaban ƙasa da ke birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Manyan Malaman Musulunci a Villa, Bayanai Sun Fito

Shugaba Tinubu ya sake tura malaman addini zuwa Nijar
Shugaba Tinubu ya amince malaman addinin musulunci su koma Nijar domin tattaunawa Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Dalilin Tinubu na sake tura malaman zuwa Nijar

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata wallafa da NTA ta yi a Twitter, ranar Alhamis, 24 ga watan Agustan 2023.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan za a tuna dai tawagar malaman addinin musuluncin sun je Nijar a karon farko, domin tattaunawa da shugaban gwamnatin sojojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani.

Hukuncin na Shugaba Tinubu ya yanke shi ne a matsayinsa na shugaban ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS).

Janar Tchiani, wanda shi ne shugaban dakarun tsaron fadar shugaban ƙasar Nijar, ya hamɓarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

A yayin ziyarar malaman karo na farko dai malaman sun tattauna sosai da sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin Bazoum, inda suka nuna a shirye su ke da su hau kan teburin sulhu da ƙungiyar ECOWAS.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wike Ya Bayar Da Umarnin Cafke Mamallakin Benen Da Ya Rufto a Birnin Tarayya Abuja

An nuna malaman kan hanyarsu ta zuwa Nijar

A wani faifan bidiyo da Salihu Baban Takko ya sanya a Facebook, ya nuna tawagar malaman addinin cikin jirgi suna kan hanyarsu ta zuwa birin Yamai na Nijar.

Tawagar malaman dai ƙunshe take da malaman addinin musulunci waɗanda za su tattauna da gwamnatin sojojin ta Jamhuriyar Nijar.

Sojoji Ba Za Su Ba Bazoum Mulki Ba

A wani labarin kuma, shugaban tawagar masu shiga tsakani na ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS), Janar Aɓdulsalami Abubakar, ya bayyana cewa sojojin sun ce ba za su mayar da Shugaba Bazoum kan mulki ba.

Janar Abdulsalami ya bayanin cewa sojojin sun bayyana cewa sun shirya tattaunawa kan komai amma banda batun mayar da Bazoum kan mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng