Godwin Emefiele Bai Halarci Zaman Kotu Ba, Bayanai Sun Fito
- Shari'ar dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele ta ƙara samun tangarɗa bayan ba a cigaba da sauraron ƙarar ba
- An dakatar da gurfanar da Godwin Emefiele ne bisa rashin sanya ƙararsa cikin jerin ƙararrakin da kotun za ta saurara a yau
- Haka kuma Emefiele da wacce ake ƙararsu tare, Sa'adatu Ramalan Yaro, da lauyoyinsu duk ba su halarci kotun ba domin cigaba da sauraron shari'ar
FCT, Abuja - An sake dakatar da gurfanar da dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele.
Ana tuhumar Emefiele da cin hanci da rashawa da almundahanar kuɗi tare da Sa’adatu Ramallan Yaro.
Emefiele bai halarci kotu ba
Kamar yadda The Nation ta rahoto, ba a karanto ƙarar Emefiele ba cikin ƙararrakin da za a saurara a safiyar yau, sannan dakataccen gwamnan na CBN da Yaro ba su halarci kotun ba.
"Akwai Babbar Matsala" Fitaccen Malami Ya Bayyana Hukuncin da Kotu Zata Yanke Kan Nasarar Tinubu a 2023
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An tattaro cewa ba a ga jami'an tsaro masu yawo sun yi dafifi a kotun ba, sannan lauyoyin duka ɓangarorin ba su halarci kotun ba.
Mai shari'a Hamza Muazu, wanda ya tafi hutu shi ne ya ɗage sauraron ƙarar a satin da ya gabata.
FG na tuhumar Emefiele kan badaƙalar N6.9bn
Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Godwin Emefiele ne tare da Sa'adatu Ramalan Yaro bisa zargin haɗa baki wajen yin sama da faɗi da dukiyar ƙasa.
Gwamnatin tarayyaar dai tana tuhumar dakataccen gwamnan babban bankin ne tare da Sa'adatu wacce babbar ma'aikaciya ce a bankin, kan wajen haɗa baki tare inda suka salwantar da N6.9bn.
An gurfanar da Emefiele a gaban kotun ne bayan gwamnatin tarayyar ta janye tuhumar da take yi masa kan mallakar makamai ba bisa ƙa'ida.
Yan Uwan Emefiele Sun Janye Kara
A wani labarin kuma na daban, kun ji cewa ƴan uwan dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, sun janye ƙarar da suka shigar da hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS).
Ƴan uwan na Emefiele wato Emefiele George Emefiele da Edanta Emefiele, sun shigar da ƙarar ne bisa zargin hukumar da take musu haƙƙi a.lokacin da take gudanar da binckenta kan Emefiele.
Asali: Legit.ng