Gwamna Zulum Ya Gwangwaje Sojojin Da Suka Ji Rauni Da Kyautar Kudi Miliyan 10
- Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno ya yi wa dakarun rundunar sojojin Najeriya sha tara ta arziki
- Domin ragewa gwamnonin da suka jikkata a filin daga radadi, Zulum ya ba su tallafin kudi naira miliyan 10
- Gwamnan ya kuma jinjinawa dakarun sojin kasar kan yadda suke kare martabar Najeriya da kuma wanzar da zaman lafiya a jihar Borno da ke fama da ta'addanci
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Borno - Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya amince da sakin naira miliyan 10 a matsayin tallafi domin ragewa sojojin da suka ji rauni yayin yaki da ta'addanci a jihar radadi, jaridar Punch ta rahoto.
Wannan tallafi alkawari ne da Gwamna Zulum ya daukarwa sojojin watanni biyu da suka gabata a wajen taron cin abincin sallah wanda shugaban hafsan soji, Manjo Janar Taoreed Lagbaja ya shirya.
Tallafin miliyan 10 ya shiga hannun sojoji a Borno
Kwamishinan labarai da tsaron cikin gida na jihar, Farfesa Usman Tar, da taimakon sakataren dindin, Mustapha Busuguma sun gabatar da kyautar gwamnan ga kwamandan sashi na 7 na rundunar sojojin Najeriya, Manjo Janar Peter Malla a hedkwatar rundunar da ke Maiduguri a ranar Asabar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Tar ya ce:
"Mun zo nan ne don cika alkawarin da mai girma gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya dauka.
"Za ku iya tuna cewa gwamnan ya kasance a nan a ranar Sallah don halartan wani taro, wanda a lokacin ya nuna jajircewar gwamnatin jihar Borno kan jin dadin dakarunmu sannan ya yi alkawarin bayar da tallafin naira miliyan 10 ga sojojin da suka ji rauni. A safiyar nan ya aiko mu domin mu zo mu kawo wannan kyauta."
Sojoji sun sha jinjina a jihar Borno
Ya kuma jijinawa rundunar sojoji kan kare martabar Najeriya da kuma wanzar da zaman lafiya a jihar ta Borno.
Da yake karbar tallafin, GOC na rundunar sashi na 7, Malla ya nuna godiya ga Gwamna Zulum a kan wannan karamci da ya yi masu, rahoton Peoples Gazette.
Boko Haram sun farmaki Borno, sun sace mata 7
A wani labari na daban, mun ji cewa wasu da ake zaton yan ta'addan Boko Haram ne sun farmaki wasu ayarin motoci dauke da kayayyaki da fasinjoji a karamar hukumar Bama ta jihar Borno, inda suka kashe mutum biyar da sace mata bakwai.
Sun kai hari ne a ranar Alhamis a kan ayarin motocin jami’an tsaro da ke raka motocin fasinja da kayayyaki kusa da garin Banki da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru a karamar hukumar da misalin karfe 2:30 na rana.
Asali: Legit.ng