Mahaifiyar Shahararren Mawakin Najeriya Wizkid Ta Riga Mu Gidan Gaskiya
- Allah ya yi wa mahaifiyar fitaccen mawakin Najeriya, Ayodeji Balogun wanda aka fi sani da Wizkid rasuwa
- Misis Jane Dolapo Balogun ta rasu ne a ranar Juma'a 17 ga watan Agustan shekarar 2023 kamar yadda manajan Wizkid ya tabbatar
- Misis Balogun tana da yara biyu Yetunde Balogun da Lade Balogun baya ga fittacen mawakin Ayodeji Balogun
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani labari mai sosa zuciya ya mamaye masana'antar mawakan Najeriya a yayin da aka rahoto cewa fitaccen mawaki Ayodeji Balogun ya rasa mahaifiyarsa, Jane Dolapo.
A cewar rahoto da fitaccen shafin watsa labarai na Instagram, Goldmyne, mahaifiyar Wizkid, Jane ta rasu a ranar Juma'a, 18 ga watan Agustan 2023.
A halin yanzu ba a san abin da ya yi sanadin mutuwarta ba kuma ba a bayyanawa al'umma ba.
Fitccen mawakin wanda ya lashe lambobin yabo da dama bai riga ya ce komai kan rahoton ba. Amma a cewar Goldmyne, wani na kusa da Wizkid ya bayyana musu cewa Misis Balogun ta yi bankwana da duniya kuma ta rasu a safiyar ranar Juma'a.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Duba rahoto dangane da rasuwar mahaifiyar na Wizkid a kasa:
Manajan Wizkid ya tabbatar da rasuwar mahaifiyar
Da ya ke tabbatarwa The Punch afkuwar lamarin, Sunday Aare, tsohon wanda ke kula da Wizkid ya ce Misis Balogun ta rasu da asubahin ranar Juma'a.
"Eh, ta rasu a safiyar yau, misalin karfe 1.30," in ji Aare.
Marigayin kuma tana wasu yaya biyu da suka hada da Yetunde Balogun da Lade Balogun.
Duba yadda wasu a soshiyal midiya suka yi martani game da rasuwar mahaifiyar Wizkid
@iam_tonyteddy:
"Ki huta mama."
@obaksolo
"Ya Allah."
@batool_bello:
"Allah ya gafarta mata ya saka mata da Aljanna Firdaus."
@ayomidate:
"Toh fa, wannan ba gaskiya bane."
@da_king_m:
"Wannan abin bakin ciki ne ... Allah ya jikan mama, amen."
@bimbola180:
"Abin bakin ciki Allah ya jikanta."
@okwudili_omotikogiveafuck:
"Kuma matar ba wani tsufa ta yi ba fa. Kai mutuwa. Allah ya jikan mama."
Asali: Legit.ng