Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Babban Sakataren Fadar Shugaban Kasa

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Olusesan Olufunso Adebiyi daga jihar Ekiti a matsayin sabon babban sakataren fadar shugaban ƙasa
  • Adebiyi ya maye gurbin Tijjani Umar, wanda ya riƙe muƙamin tun daga ranar 5 ga watan Afirilun 2020, har zuwa ritayarsa a ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta
  • Babban sakataren ya fara aiki ne a ranar Litinin, 14 ga watan Agusta inda ya yi alƙawarin bayar da gudunmawarsa ga ƙasar nan

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin Olusesan Olufunso Adebiyi, a matsayin sabon babban sakataren fadar shugaban ƙasa.

A cewar wata wallafa da aka yi a shafin fadar shugaban ƙasa a Twitter, Adebiyi ya maye gurbin Tijjani Umar, wanda ya yi ritaya daga muƙamin a ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Hotuna Sun Bayyana Yayin Da Hadimin Buhari Ya Bayyana Inda Nasir El-Rufai Ya Koma Bayan Ya Hakura Da Zama Minista

Shugaba Tinubu ya nada babban sakataren fadar shugaban kasa
Shugaba Tinubu ya nada dan jihar Ekiti a matsayin babban sakataren fadar shugaban kasa Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

Umar ya kasance riƙe da muƙamin tun daga ranar 5 ga watan Afirilun 2020 har zuwa lokacin ritayarsa.

Sabon naɗin da Tinubu ya yi ya kama aiki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An tattaro cewa Adebiyi ya fara aiki ne a ranar Litinin, 14 ga watan Agusta a birnin tarayya Abuja, inda ya yi alƙawarin yin aiki tuƙuru ga Najeriya. Bikin miƙa mulkin dai an yi shi ne a fadar shugaban ƙasa da ke Aso Rock Villa a Abuja.

Adebiyi tun da farko ya riƙe muƙamin babban sakatare a ma'aikatar lafiya ta ƙasa, sannan ya nuna godiyarsa ga magabacinsa, Umar.

Adebiyi ya ɗauki alƙawarin jajircewa wajen hidimatawa ƙasar nan. Sannan ya yi bayanin cewa zai iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin wannan gwamnatin ta yi nasara.

Ya kuma sha alwashin yin dukkanin ayyukan da ke a gabansa cikin gaskiya, jajircewa da amana.

Kara karanta wannan

"Abun Kunya": 'Yan Najeriya Sun Fusata Bayan Ganin Dakarun Tsaro Na Musamman Da Ke Gadin Seyi Tinubu

Adebiyi wanda ɗan jihar Ekiti ne, an haife shi a ranar 8 ga watan Janairun 1968 a Kabba da ke jihar Kogi.

Shugaba Tinubu Na Duba Yiwuwar Dawo Da Tallafi

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya fara duba yiwuwar dawo da tallafin man fetur a ƙasar nan.

Shugaban ƙasar zai dawo da tallafin na wucin gadi ne duba da yadda ƴan Najeriya ke ta kuka kan halin matsin da ake ciki a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng