“N720 Duk Litar Fetur”, Kungiyoyin NLC Da TUC Sun Sha Alwashin Shiga Yajin Aiki Idan Aka Kara Farashin Mai
- Kungiyar kwadago ta gargaɗi gwamnatin Shugaba Tinubu kan yunƙurin siyar da man fetur kan N720 duk lita
- Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa Joe Ajaero ne ya yi wannan gargadi a wajen taron ƙungiyar a Abuja
- Gamayyar kungiyoyin NLC da TUC sun sha alwashin tsunduma ƙasar gaba ɗaya cikin yajin aiki muddun gwamnati ta yi biris da buƙatunsu
FCT, Abuja - Gamayyar ƙungiyar 'yan ƙwadago ta ƙasa ta NLC da TUC, ta sha alwashin jefa ƙasar cikin yajin aikin gama-gari.
Hakan ya biyo bayan yunƙurin da gwamnantin Tarayya take na ganin ta ƙara farashin litar man fetur a ƙasa baki ɗaya.
NLC za ta shiga yajin aiki idan aka sayar da man fetur kan N720
Kamar yadda aka wallafa a shafin AIT, ƙungiyar ƙwadagon a zaman da ta yi na ranar Litinin, ta tabbatar da cewa za ta zunduma yajin aikin gama-gari da zarar farashin fetur ya wace wanda yake a yanzu.
Juyin Mulki: Shin An Cinnawa Ofishin Jakadancin Najeriya a Nijar Wuta? Gwamnatin Tarayya Ta Yi Martani
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban NLC Joe Ajaero yayin da yake aika saƙon gargaɗin a Abuja, ya nemi gwamnati da kar ta yi wasa da buƙatun na su.
Hakan na zuwa ne dai jim kaɗan bayan wani taro da kungiyar ta ƙwadago ta yi da Shugaba Tinubu, inda aka cimma matsayar cewa za su dakatar da zanga-zangar da suka ƙuduri aniyar yi da farko.
Rashin ciniki ya sanya 'yan kasuwa siyar da gidajen mansu
A baya Legit.ng ta yi rahoto kan koken da ƙungiyar dilallan man fetur mai zaman kanta ta ƙasa (IPMAN), ta yi kan halin da mambobinta suka shiga tun bayan cire tallafi.
Ƙungiyar IPMAN ta ce da dama daga cikin mambobinta sun gaza ci gaba da kasuwanci, inda yanzu haka suka sanya gidajen man na su a kasuwa.
Fetur bai gama tashi ba, zai iya komawa N750 duk lita
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan hasashen da ƙungiyar manyan dilalan kasuwancin man fetur na Najeriya suka yi na cewar akwai yiwuwar litar man fetur ta koma naira 750.
Kungiyar dilallan wato IPMAN, ta ce hakan ya samo asali ne daga ci gaba da karyewar darajar naira a kan dala, wacce da ita ake amfani wajen shigo da man fetur daga waje.
Asali: Legit.ng