Shin An Cinnawa Ofishin Jakadancin Najeriya a Nijar Wuta? Gwamnatin Tarayya Ta Yi Martani

Shin An Cinnawa Ofishin Jakadancin Najeriya a Nijar Wuta? Gwamnatin Tarayya Ta Yi Martani

  • Ofishin jakandancin Najeriya a Nijar ya kwantar da hankula kan batun ƙona gininsa da masu zanga-zanga suka yi a ƙasar
  • Dr Liti Auwalu, babban kwamishinan ofishin jakadancin Najeriya a Nijar, ya bayyana cewa jita-jitar da bidiyoyin da ake yaɗawa ƙarya ce tsagwaronta
  • Ya buƙaci al'umma da su yi watsi da jita-jitar da bidiyoyin inda ya yi nuni da cewa ofishin jakadancin yana da cikakken tsaro

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yamai, Jamhuriyar Nijar - Ofishin jakandanci Najeriya a Jamhuriyar Nijar ya ƙaryata jita-jitar cewa an cinnawa ginin hukumar wuta a yayin zanga-zangar da aka yi a ƙasar.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban kwamishinan ofishin jakadancin, Dr Liti Auwalu, ya fitar a ranar Juma'a, 11 ga watan Agusta.

Ba a kona ofishin jakadancin Najeriya a Nijar ba
Hukumomi sun bayyana cewa ba a kona ofishin jakadancin Najeriya a Nijar ba Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Sanarwar ta ofishin jakadanci ta biyo bayan wani bidiyo da ya yaɗu yana nuna masu zanga-zanga na son kutsa wa cikin ginin 'Chancery' a birnin Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

An Bayyana Abin da Sanatoci Suka Gayawa Shugaba Tinubu Kan Fafata Yaki Da Jamhuriyar Nijar

Kamar yadda yake ƙunshe a cikin sanarwar, Auwalu ya bayyana bidiyon a matsayin na ƙarya inda ya buƙaci jama'a da su yi watsi da shi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

"Mun lura da wasu bidiyoyin ƙarya waɗanda ke nuna taɓa ginin 'Chancery' a birnin Yamai da masu zanga-zanga suka yi yana ta yawo a kafafen sada zumunta."
"Ofishin jakadancin yana son sanar da jama'a cewa duk da masu zanga-zanga sun yi ƙoƙarin shiga cikin ofishin a ranar 30 ga watan Yuli, sojojin Najeriya da jami'an ƴan sanda sun magance matsalar nan take."

Sai dai, Auwalu, ya yi nuni da cewa ofishin jakadancin yana da isashshen tsaro a ƙarƙashin sojojin Najeriya, sannan babu buƙatar tayar da hankula.

Ya kuma nanata cewa bidiyoyin da su ke yawo a soshiyal midiya na ƙarya ne sannan yakamata jama'a su yi fatali da su.

Kara karanta wannan

Hankalin Babban Gwamnan Jam'iyyar PDP Ya Tashi Bisa Zargin Yunkurin Yi Ma Sa Juyin Mulki

Sanatoci Sun Bayyana Matsayarsu Kan Yaki Da Nijar

A wani labarin kuma, sanatocin Najeriya sun bayyana matsayarsu kan shirin fafata yaƙi da Jamhuriyar Nijar.

Sanata Abdul Ningi ya bayyana cewa sanatocin sun gayawa Shugaba Tinubu cewa ya aje batun fafata yaƙi da Jamhuriyar Nijar a gefe guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng