Nijar: Kungiyar CAN Ta Ce Daukar Matakin Soji Zai Haddasa Gaba Tsakanin Najeriya Da Makwabtanta
- Kungiyar Kiristocin Najeriya ta shawarci Tinubu kan amfani da ƙarfin soji a jamhuriyar Nijar
- Kungiyar ta ce ba ta goyon bayan matakin, saboda zai iya haddasa gaba tsakanin Najeriya da maƙwabtanta
- Ta shawarci Tinubu da ECOWAS da su ci gaba da bin matakai na diflomasiyya wajen ganin sun warware rikicin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), ta yabawa shugaban Najeriya, Bola Tinubu kan ƙoƙarin da yake wajen ganin ya dawo da dimokuraɗiyya a Nijar.
Haka nan CAN ta yabawa ƙoƙarin ƙungiyar raya tattalin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), na yin adawa da juyin mulkin Nijar da take yi.
Shugaban ƙungiyar CAN na ƙasa, Archbishop Daniel Okoh ne ya yi wannan kiran a wani saƙo da ya aikawa Tinubu da ECOWAS kamar yadda rahoton Channels TV ya bayyana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
CAN ta faɗi illar amfani da ƙarfin soji kan Nijar
Daniel ya ce CAN ta goyi bayan duk ƙoƙarin da ake yi na dawo da dimokuraɗiyya a Nijar, amma sam ba ta goyi bayan amfani da ƙarfin soji ba.
Ta ce yin amfani da ƙarfin soji zai iya haifar da ƙiyayya da gaba mai tsanani a tsakanin Najeriya da maƙwabtanta.
A domin hakan ne CAN ta shawarci Shugaba Tinubu, da ya ci gaba da bin duk wasu hanyoyi na maslaha, wajen ganin ya warware rikicin ba tare da yin abinda zai ɓata alaƙar ƙasashen biyu ba.
Kungiyar ECOWAS na ganawa a Abuja
Legit.ng ta kawo rahoto cewa a yanzu haka ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), na gudanar da zamanta yau Alhamis a Abuja.
Yanzu-Yanzu: ECOWAS Ta Sake Sanya Sabbin Takunkunmi Kan Juyin Mulkin Jamhuriyar Nijar, Bayanai Sun Fito
Zaman da ke gudana ya biyo bayan cikar wa'adin da ƙungiyar ta ECOWAS ta bai wa sojojin Nijar na su mayar da mulki hannun Muhammed Bazoum.
ECOWAS dai na ƙoƙarin bin duk wasu matakai na diflomasiyya wajen ganin ta warware rikicin na Nijar, sai dai har yanzu ba ta cire ran amfani da ƙarfin soji ba.
Ana sa ran ƙungiyar ta ECOWAS za ta sanar da sabbin matakan da za ta ɗauka kan sojojin na Nijar a wannan zaman na ranar Alhamis.
Sojojin Nijar sun naɗa sabon Firaminista
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan naɗin sabon firaministan da zai jagoranci Nijar da sojojin ƙasar suka yi.
Sojojin sun sanar da naɗin Ali Mahaman Lamine a matsayin sabon firaminista, biyo bayan yin biris da matakin ECOWAS da suka yi.
Asali: Legit.ng