SERAP Za Ta Shigar Kara Kan Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio

SERAP Za Ta Shigar Kara Kan Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio

  • Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya shiga sabuwar matsala kan batun kuɗin shaƙatawar sanatoci
  • Ƙungiyar SERAP, a cikin wata sanarwa ranar Alhamis, ta bayyana cewa za ta shigar da shugaban majalisar ƙara kan kalaman da ya yi
  • Akpabio, a lokacin zaman majalisar na ranar Laraba ya bayyana cewa an tura wa Sanatoci kuɗi domin su ji daɗin hutun su, amma daga baya ya janye kalamansa

FCT, Abuja - Ƙungiyar SERAP ta sanar da cewa za ta shigar da ƙara kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, bisa kalaman da ya yi na biyan kuɗin shaƙatawa ga sanatoci.

A lokacin zaman majalisar na ranar Laraba, 9 ga watan Agusta, Akpabio ya bayyana cewa an tura wa sanatocin kuɗi domin su ji daɗin hutun su, amma daga baya ya janye kalamansa inda ya ce addu'o'i aka tura musu.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Bukaci Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio Ya Gaggauta Yin Murabus

SERAP ta maka Akpabio kara
SERAP za ta kai karar Godswill Akpabio Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Yadda Akpabio ya bayyana kuɗin shaƙatawar sanatoci

Shugaban majalisar dattawan ya bayyana cewa:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Domin mu samu damar jindaɗin hutun mu yadda yakamata, magatakardan majalisa ya tura wa kowannen mu kuɗi a asusunsa."

Kalaman na Akpabio ya janyo ƴan Najeriya sun yi ta caccakarsa a soshiyal midiya, waɗanda suka yi ƙorafin cewa ƴan majalisar na ta bushasha da kuɗi a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da shan wahala a sakamakon cire tallafin man fetur.

Dalilin da ya sa SERAP ta kai ƙarar Akpabio kotu

Biyo bayan Allah wadai da kalaman na Akpabio, SERAP a cikin wata sanarwa a shafinta na Twitter a ranar Alhamis, 10 ga watan Agusta, ta bayyana cewa za ta shigar da shugaban majalisar dattawan ƙara a gaban kotu.

Sanarwar na cewa:

Kara karanta wannan

Bidiyon Akpabio Yana Sanar Da Cewa An Tura Wa Yan Majalisa Kudaden Shakatawa Yayin Hutu Ya Janyo Cece-Kuce

"Za mu shigar da ƙara kan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, bisa zargin biyan kuɗin shaƙatawa da magatakardan majalisa ya yi ga asusun sanatoci, yayin da wasu ƴan Najeriya miliyan 137 ke fuskantar matsin tattalin arziƙi."

An Bukaci Akpabio Ya Yi Murabus

A wani labarin kuma, wani ɗan gwagwarmaya mai rajin kare dimokuraɗiyya ya buƙaci shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da ya gaggauta yin murabus.

Timi Frank ya yi wannan kiran ne bayan bayyana bidiyon katoɓarar da Akpabio ya yi kan gwangwaje sanatoci da kuɗi domin su ji daɗin hutun su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng