'Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane 17 a Wani Hari Da Suka Kai a Jihar Filato

'Yan Bindiga Sun Sake Kashe Mutane 17 a Wani Hari Da Suka Kai a Jihar Filato

  • Wasu 'yan bindiga ɗauke da manyan makamai sun kai hari a ƙaramar hukumar Barikin Ladin jihar Filato
  • A yayin harin, 'yan bindigar sun halaka aƙalla mutane 17 a garin Heipang da asubahin ranar Alhamis
  • Rundunar 'yan sandan jihar ta tura da jami'anta wurin da wannan mummunan lamarin ya faru don ɗaukar matakan da suka dace

Filato - Wasu ‘yan bindiga sun sake kai hari, inda suka kashe mutane 17 a ƙaramar hukumar Barkin Ladi da ke jihar Filato.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa, an kai harin ne a garin Heipang da ke ƙaramar hukumar cikin daren Laraba, wayewar garin ranar Alhamis.

'Yan bindiga sun halaka mutane 17 a Filato
'Yan bindiga sun sake kai hari jihar Filato, sun halaka mutane 17. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Yadda harin 'yan bindigan ya kasance

Wani mazaunin Heipang mai suna Julius Pam, wanda harin ya rutsa da 'yan uwansa ya shaidawa manema labarai yadda lamarin ya kasance.

Kara karanta wannan

Jarumin Gwamna Ya Jagoranci Jami’an Tsaro An Dura Gungun ‘Yan ta’adda Cikin Dare

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya tabbatar da cewa 'yan ta'addan sun shigo ne da asubahin ranar Alhamis, inda suka halaka mutane 17 ciki kuwa har da ɗan uwansa, matarsa da kuma yaransu.

Wata majiya mai ƙarfi a ofishin rundunar 'yan sandan jihar ta Filato, ta tabbatar da cewa tuni aka tura jami'ai zuwa yankin da lamarin ya faru.

Gwamnan Filato ya ƙaddamar da cibiyar tattara bayanai

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang, ya ƙaddamar da wata cibiyar tattara bayanai ta tsaro domin bai wa mutane damar sanar da jami'ai halin da suke ciki.

Gwamnan ya ce cibiyar ta samar da wata lambar waya da mutane za su iya kira a kyauta domin ba da bayanai na tsaro a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.

Ya ƙara da cewa hakan zai taimakawa gwamnatin jihar wajen samun bayanai da za su ba ta damar ɗaukar matakai na gaggawa a duk lokacin da aka fuskanci wata matsala ta tsaro.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Dakile Yunkurin 'Yan Ta'adda, Sun Ceto Mutane 5 Da Aka Yi Garkuwa Da Su a Katsina

Jihar Filato na fama da ƙaruwar hare-haren 'yan bindiga, wanda ko a kwanakin baya sai da jaridar This Day ta kawo rahoton mutane 10 da 'yan ta'adda suka kashe a ƙananan hukumomin Riyom da Jos ta Kudu.

Sai dai a lokuta da dama, jami'an tsaro kan yi nasarar halaka da yawa daga cikin 'yan ta'addan a farmake-farmake da suke kai musu.

'Yan bindiga sun sace mutane 14 a jihar Katsina

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wasu mutane 14 da 'yan bindiga suka sace a wasu ƙauyuka uku na jihar Katsina yayin wani hari da suka kai.

Miyagun 'yan bindigar dai sun aikata wannan mummunar ta'asar ne a ƙauyukan uku da ke ƙaramar Sabuwa ta jihar Katsina.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng