Dakarun Sojoji Sun Dakile Harin Mayakan ISWAP, Sun Sheke 'Yan Ta'adda Masu Yawa
- Dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara akan mayaƙan ƙungiyar ƴan ta'addan ISWAP da suka addabi al'ummar jihar Borno
- Dakarun sojojin na atisayen 'Operation Hadin Kai' sun samu nasarar daƙile wani hari da mayaƙan na ISWAP suka kawo musu a jihar Borno
- Bayan tura ƴan ta'adda masu ɗumbin yawa zuwa barzahu, dakarun sojojin sun kuma ƙwato makamai a hannun miyagun ƴan ta'addan
Jihar Borno - Dakarun sojojin rundunar tsaro ta ƙasa da ƙasa (MNJTF) sashe na uku na atisayen 'Operation Hadin Kai' sun halaka mayaƙan ƙungiyar ƴan ta'addan Islamic State West Africa Province (ISWAP) a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun sheƙe ƴan ta'addan ne masu yawa bayan sun daƙile wani hari da suka kawo musu a Mongonu cikin jihar Borno.
Dakarun sojoji sun daƙile harin mayaƙan ISWAP
An tattaro cewa mayaƙan na ISWAP waɗanda su ke akan motocin yaƙi da babura sun farmaki dakarun sojojin dake yankin Marte a Monguno a ranar Asabar, 5 ga watan Agusta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Nan da nan musayar wuta ta kaure a tsakanin sojojin da ƴan ta'addan na ISWAP wacce aka kusan shafe mintuna 30 ana fafatawa.
Majiyoyin sirri sun gayawa Zagazola Makama, wani masanin tsaro kan yankin tafkin Chadi cewa dakarun sojojin sun daƙile harin cikin nasara inda suka halaka ƴan ta'addan masu yawa, yayin da wasu suka ranta ana kare.
Majiyoyin sun bayyana cewa an kwato kayayyakin faɗa masu yawa a hannun ƴan ta'addan ciki har da gurneti, yayin da wani soja guda ɗaya ya samu rauni a ya yin farmakin.
Idan ba a manta ba dai mayaƙan ISWAP sun sha alwashin riƙa kai farmaki a Monguno duk bayan sati biyu, bayan dakarun sojoji sun fatattake su daga garin.
'Yan Ta'adda Sun Halaka Masunta a Borno
A wani labarin kuma ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun salwantar da rayukan masunta masu yawa a yankin tafkin Chadi a iyakar Najeriya da ƙasar Kamaru.
Ƴan ta'addan sun yi wa masuntan yankan rago ne sannan suka yi awon gaba da wasu masu yawa daga cikinsu bayan sun zarge su da zama ƴan leƙen asirin dakarun sojoji.
Asali: Legit.ng